Zamfara: Sabon rikici ya barke tsakanin gwamna Matawalle da Mataimakinsa kan N31bn
- Hadimin mataimakin gwamnan Zamfara ya kalubalanci Matawalle kan ya yi bayanin yadda aka yi da Biliyan N31bn na wata 31
- Ya ce gwamnan da hadimansa a gwamnati sun karbi makudan kudade tun farkon gwamnati kan tsaro da sauran su
- Tsagin Matawalle ya maida martanin cewa idan har suna da hujja to su garzaya inda ya dace su shigar da korafi
Zamfara - Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, da mataimakinsa, Barista Mahdi Gusau, sun fara musayar yawu kan karkatar da kuɗaɗen al'umma.
Daily Trust ta rahoto cewa Sakataren Gusau, Aminu Umar, ya kalubalanci Matawalle ya fito ya yi wa al'umma jawabin yadda ya kashe biliyan N31bn waɗan da ya karba a watanni 31.
Umar ya bukaci gwamnan ya yi bayani dalla-dalla kan yadda ya tafiyar da kuɗaɗen da aka ware masa na tsaro, kasafin Ofishinsa, Sakatarensa, da kuma gidan gwamnati tun da ya hau mulki.
Haka nan kuma ya ce tun farkon kafa gwamnati, gwamna na karban miliyan N600m na tsaro duk wata, miliyan N350m tsabar kuɗin Ofishinsa, Miliyan N30m na ofishin PPS da kuma N30m na kasafin fadar gwamnati.
A cewarsa kuɗin sun kama naira Biliyan N1.1bn duk wata, wanda idan ka nunka sau 31, kuɗin sun zama Biliyan N31.3bn.
Menene martanin gwamnan?
Da yake martani kan maganar, kakakin gwamna Bello Matawalle, Zailani Bappa, ya yi fatali da zargin, inda yace Farfaganda ce kawai suke yi.
Ya ce:
"Idan suna da kwakkwaran shaida su rubuta korafi kan mai girma gwamna su gabatar wa hukumomin dake da alhaki Wannan zancen na su na nuna cewa kasala ta hana su gano gaskiya."
"Uban gidansu na daga cikin waɗan da suka tafiyar da harkokin gwamnati na shekaru biyu da rabi, meyasa ba su tattaro lamarin ba tun a baya?"
Dalilin jinkirta taron gangamin APC: Tsohon gwamna ya ce Buni ne ya jawo, yana son ya gaji Buhari a 2023
Ina aka kwana kan batun tsige Gusau?
A halin da ake ciki, kwamitin mutum Bakwai da aka kafa domin bincikar zargin da ake wa mataimakin gwamna dake barazana da kujerarsa ya fara zama.
Sakataren kwamitin, Sani Tsafe, ya tabbatar da cewa ya sauke duk wani nauyi na sanar da mataimakin gwamna da matakan da ya dace.
A wani labarin kuma Majalisar Dokoki ta tsige mataimakin kakaki, yan majalisu biyu sun sauya sheka zuwa APC
Majalisar dokokin jihar Ebonyi ta bayyana murabus ɗin mataimakin kakaki da wasu mambobinta biyu a zaman Litinin.
Sai dai lamarin ya tada hatsaniya, yayin da mutanen uku baki ɗaya suka musanta ikirarin majalisa, suna nan daram a matsayin su.
Asali: Legit.ng