Babbar magana: Bugagge ya zuba omo a ledar ruwan maganin majinyaci, ya gamu da fushin alkali
- Kotu a kasar waje ta yankewa wani bugagge hukuncin daurin shekaru uku bisa laifin yunkurin kashe majinyaci
- Rahoton da muke samu ya bayyana cewa, bugaggen ya zuba ruwan omo ne a cikin ledar ruwan magani
- Kotun ta bayyana cewa, dama a baya an sha samun mutumin da aikata laifukan da suka shafi jefa mutane a hadari
Daejeon, kasar Koriya ta Kudu - An yanke wa wani mutum dan shekaru 32 hukuncin daurin shekaru uku a gidan yari bisa laifin zuba ruwan omo a ledar ruwan maganin wani majiyyaci yayin da yake kwance a asibiti don jinyar kuna.
Majiyoyi sun bayyana a ranar Talata cewa mutumin ya aikata laifin ne a wani asibiti da ke Daejeon, mai tazarar kilomita 160 Kudu da birnin Seoul, a watan Maris din shekarar 2021.

Kara karanta wannan
Shiga tashin hankali: Abba Kyari da jiga-jigai 6 da suka fada rashin lafiya yayin bincikarsu

Asali: UGC
Bayan saka sinadarin, majiyyacin ya koka da jin ciwon kirji wanda ya kai ga wata ma'aikaciyar jinya ta canza ruwan ledan, amma mutumin ya sake zuba ruwan omon a bayan sa'a daya, in ji majiyoyin.
Wanda ake zargin da a buge yake a lokacin, ya yi ikirarin cewa omon zai kashe kwayoyin cuta tare da tsaftace hanyoyin jini, inji rahoton The Nation.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Yana da tarihin aikata laifuka a can baya, ciki har da karyawa da shiga wuraren da ba nasa ba a cikin maye a watan Agustan 2020 da kuma zubar da iskar gas a gaban gidan wani.
Pulse Nigeria ta tattaro a rahotonta cewa kotun gundumar Daejeon ta ce:
"Ya kamata a hukunta wanda ake tuhuma da aikata mummunan laifi kamar yadda ya zuba guba ga wanda ke barci ta hanyar hada omo da ruwan maganin IV."

Kara karanta wannan
Kano: Ya Jefa Yaro Cikin Rijiya Bayan Yin Rikici Da Mahaifin Yaron, Kotu Ta Ce a Tsare Shi a Gidan Gyaran Hali
Dadi kamar kifi da kaza: Jama'a sun kadu ganin shahararriyar mawakiya na cin kyankyaso
A wani labarin, wata mata daga Dar es Salaam a kasar Tanzaniya, ta zama maudu'in tattaunawa a Intanet yayin da aka gano tana kiwon kyankyasai don samun abinci.
Saumu Hamisi, wata mawakiya mai suna Ummy Doll, ta ce mutane sun yi ta maganganu da yawa a lokacin da suka ji tana ajiye kwarin domin ta ci soye.
A cewarta:
"Wasu sun ce ni mahaukaciya ce amma kyankyasai suna kawo min kudi don haka ban damu da ra'ayin mutane ba."
Asali: Legit.ng