An fidda matsaya: Jam'iyyar APC ta tura kujerar shugabancin jam'iyya ga yankin Arewa
- Bayan zama da shugaba Buhari, jam'iyyar APC ta amince da ba dan Arewa kujerar shugabancin APC
- Jiga-jigan APC sun zauna a yau Talata don tsayar da wasu maganganu da suka shafi jam'iyyar a babban birnin tarayya
- Wannan na zuwa ne jim kadan bayan da jam'iyyar ta dage taron gangaminta na kasa zuwa watan Maris
FCT, Abuja - Jam’iyyar APC mai mulki ta tura kujerar shugabancin jam'iyya ga yankin Arewa gabanin zaben 2023 mai zuwa.
Gwamna Nasiru El-Rufai (Kaduna) da Atiku Bagudu (Kebbi), ne suka bayyana hakan a lokacin da suke amsa tambayar jaridar Daily Trust a wani taron manema labarai da suka gudanar bayan ganawa da shugaba Buhari game da lamurran jam'iyyar.
El-Rufai ya ce jam’iyyar ta amince da sauya mukaman da ba kowa akansu a kwamitin ayyuka na kasa (NWC) ga tsakanin sassan Arewa da Kudancin kasar nan gabanin taron gangamin jam'iyyar APC na kasa na ranar 26 ga Maris.
Kenan za a iya cewa, mukamin shugabancin jam'iyyar wanda tsohon Gwamna John Odigie-Oyegun da Adams Oshiomhole na Jihar Edo daga yankin Kudu suka rike zai koma yankin Arewa.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
El-Rufai ya ce:
"Mun amince da tsarin shiyya-shiyya ga dukkanin shiyyoyin siyasar kasar nan guda shida kuma da gaske, mun sauya mukaman. Shiyyoyin Arewa za su dauki mukaman da shiyyoyin Kudu ke rike dasu a shekaru takwas da suka wuce, da kuma akasin haka.
“Don haka, tsari ne mai sauki sosai, daidai kuma shi ne adalci. Yanzu za mu koma mu duba a matakin shiyya, mu duba mukaman da ake da su kuma za a fara shirye-shiryen taron da gaske. Don haka da yardar Allah ranar 26 ga Maris za mu yi taron gangami na kasa.”
Hakazalika, Daily Trust ta rahoto El-Rufai na cewa, babu sabani tsakanin gwamnonin jam'iyyar ta APC a yanzu.
Takaitaccen taron da ya gudana a zauren majalisar fadar shugaban kasa a Abuja ya samu halartar mutane kamar mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo da gwamnoni 19.
Gwamnonin sun hada da na Yobe, Kano, Kogi, Ekiti, Nasarawa, Kwara, Ebonyi, Jigawa, Lagos, Imo. Ogun, Borno, Niger, Gombe, Osun, Kebbi, Plateau, da kuma mataimakin gwamnan jihar Anambra wanda ya bar jam’iyyar APGA zuwa APC a bara.
Dalilin jinkirta taron gangamin APC: Tsohon gwamna ya ce Buni ne ya jawo, yana son ya gaji Buhari a 2023
A wani labarin, wani tsohon gwamnan wanda ya kasance cikin wadanda suka kafa jam’iyyar All Progressives Congress (APC), ya zargi Gwamna Mai Mala Bunin a jihar Yobe da son a yi taron gangamin jam’iyyar da zaben fidda gwanin shugaban kasa na 2023 a rana guda.
Da yake martani kan rikicin da ya dabaibaye jam’iyyar mai mulki kan taronta, tsohon gwamnan ya bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya gaggauta daukar mataki saboda ra’ayin APC, Daily Trust ta rahoto.
Bayan an kai ruwa rana, jam’iyyar mai mulki ta sanar da ranar 26 ga watan Maris a matsayin ranar babban taronta na kasa.
Asali: Legit.ng