Kano: 'Yan sanda sun damke matashin da ya yaga Qur'ani tare da taka shi

Kano: 'Yan sanda sun damke matashin da ya yaga Qur'ani tare da taka shi

  • Rundunar 'yan sandan jihar Kano ta tabbatar da damke wani matashin maigadi da ake zargi da yagawa tare da taka Al-Qur'ani
  • Kamar yadda aka tattaro, mummunan lamarin ya auku a ranar Lahadi a yankin Kuntau kuma da kyar ya sha sakamakon yunkurin kone shi da jama'a suka yi
  • Dan uwan wanda matashin ke wa gadi ya sanar da cewa ya tarar da jama'a da miyagun makamai za su halaka shi kafin jami'an Hisbah su kai dauki

Kano - Wani matashin maigadi wanda har yanzu ba a san sunansa ba, ya na hannun hukumar 'yan sanda ta jihar Kano kan zarginsa da ake yi da yaga Qur'ani tare da take wani sashinsa.

Wanda ake zargin, ya kubuta daga babbaka shi da ranshi da jama'ar yankin Kuntau a birnin Kano suka yi niyya bayan isar jami'an hukumar Hisbah wurin.

Kara karanta wannan

'Yan fashi sun kacame da rikici suna tsaka da fashi, sun halaka junansu da makamansu

Kano: 'Yan sanda sun ceci matashin da ya yaga Qur'ani, kiris da jama'a sun babbaka shi
Kano: 'Yan sanda sun ceci matashin da ya yaga Qur'ani, kiris da jama'a sun babbaka shi. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Daga bisani jami'an Hisbah sun mika shi hannun 'yan sanda kuma a halin yanzu an tsare shi inda ake cigaba da bincike.

Wani dan uwan mamallakin gidan da matashin ke gadi mai suna Sunusi Ashiru, ya sanarwa da Daily Trust cewa an tabbatar masa da kyar matashin ya kubuta.

Ya ce: "Ba na nan lokacin da ya aikata amma na dawo na tarar da jama'a dauke da makamai daban-daban suna kokarin halaka shi.
"A yayin da na tambaya, sun yi min bayanin abinda yayi kuma a lokacin ne jami'an hukumar Hisbah suka kama shi tare da mika shi hannun 'yan sanda."

Al'amarin ya faru ne a ranar Lahadi kamar yadda Daily Trust ta tattaro.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa, ya tabbatar da aukuwar lamarin kuma ya ce wanda ake zargin ya na hannun 'yan sanda.

Kara karanta wannan

NDLEA ta cafke kudi har $4.7 na jabu a Abuja, ta yi ram da maijego dauke da kwayoyi

Ya dauka alkawarin bayyana karin bayan tare da abinda ya faru bayan bincike ya kankama.

Zargin kona Al-Kur'ani: Fusatattun jama'a sun babbaka wani mutum a Pakistan

A wani labari na daban, fusatattun jama'a sun kashe wani bawan Allah da ake zargi da kone Al-Qur'ani mai girma a kasar Pakistan.

An gano cewa jama'an sun lakada masa mugun duka tare da kona shi a garin mai suna Khanewal da ke lardin Punjab a kasar Pakistan, Aminiya Daily Trust ta wallafa.

Jama'a masu yawa ne a halin yanzu aka tabbatar da an kama su sakamakon hannunsu a kisan. Lamarin ya auku a ranar Asabar, kamar yadda Firayim minsitan kasar na harkokin addini, Tahir Ashrafi ya sanar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng