Innalillahi: Kwamishinan hukumar zabe na Zamfara, Gazura, ya gwabza hatsari, ya rasu
- Kwamishinan hukumar zabe mai zaman kanta na jihar Zamfara, ZASIEC, Hashimu Shehu Gazura ya riga mu gidan gaskiya
- Gazura wanda ya taba wakiltar mazabar Gummi ta 2 a majlisar jihar, ya rasu ne sakamakon hatsarin da ya yi a kan titin Yawuri
- Kamar yadda shugaban hukumar majalisar jihar, Mansur Bungudu ya sanar, ya ce za a yi jana'izarsa a ranar Asabar a fadar sarkin Gummi
Zamfara - Hashimu Shehu Gazura, kwamishinan hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Zamfara, ZASIEC, ya gwabza hatsarin mota kuma ya rasu.
Hatsarin ya auku ne kan titin Yawuri da ke jihar Kebbi a ranar Juma'a kamar yadda TheCable ta ruwaito.
Mansur Bungudu, shugaban hukumar majalisar jihar Zamfara, ya sanar da rasuwar Gazura a wata takarda da ya fitar a ranar Asabar.
"Ya rasu ne a ranar Juma'a sakamakon mummunan hatsarin da ya gwabza a kan titin Yawuri na jihar Kebbi," takardar tace.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Za a yi jana'izar mamacin a fadar Sarkin Gummi a ranar Asabar da karfe 11 na safe."
TheCable ta ruwaito cewa, Gazura tsohon dan majalisar jihar Zamfara ne wanda ya taba wakiltar mazabar Gummi ta 2.
Masu garkuwa sun kashe tsohon mai neman takarar gwamnan Zamfara a hanyar Abuja zuwa Kaduna
A wani labari na daban, 'yan bindiga sun kashe Sagir Hamidu, tsohon mai neman takarar gwamnan Zamfara a shekarar 2019, a babban hanyar Abuja zuwa Kaduna. Marigayin dan siyasan ya nemi kujerar gwamnan ne a karkashin jam'iyyar All Progressives Congress, APC mai mulkin kasa.
Maharan sun bindige shi har lahira ne yayin da suka bude wuta kan matafiya a kusa da Rijana misalin karfe 4 na yammacin ranar Lahadi.
Majiya daga jami'an tsaro da suka nemi a boye sunansu sun tabbatar wa Daily Nigerian mutuwarsa suna mai cewa, 'yana daga cikin wadanda suka mutu sakamakon harbin da yan bindigan suka yi.'
Majiyoyi sun ce an bindige fasinjoji da dama da suke nemi su tsere, yayin da wadanda suka bada hadin kai su kuma an tisa keyarwasu zuwa cikin daji.
Wani da ya tsira daga harin kuma ya nemi a boye sunansa ya shaidawa wakilin Daily Nigerian cewa harin ya faru ne a kusa da Rijana.
Ya ce: "Masu garkuwar sun yi amfani da rashin kyawun hanyar, wanda hakan ya tilastawa motocci tafiya a hankali kuma a hannu guda a titin."
Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Kaduna, Mohammed Jalige bai amsa kirar da aka masa ba har zuwa lokacin hada wannan rahoton.
Asali: Legit.ng