Yan bindiga sun sake kai kazamin hari jihar Benuwai, Sun halaka mutane
- Yan bindiga sun halaka aƙalla mutum 5 a wani sabon hari da suka kai yankin karamar hukumar Gwer West a jihar Benuwai
- Bayanan da muka samu daga wani shaidan gani da ido, yace maharan sun kashe mutum 4 a kauyen Tse Udeghe, ɗaya kuma a hanyar Makurdi
- Shugabar karamar hukumar Gwer ta ce gwamnatinta ta ba da kyautar motoci 10 ga sojoji don kara karfin tsaro a yankin
Benue - Akalla mutum biyar aka tabbatar sun mutu a wani sabon hari da yan bindiga suka kai ƙauyen, Tse Udeghe dake karamar hukumar Gwer West a jihar Benuwai.
Wani shaidan gani da ido ya bayyana cewa mutane da yawa sun samu raunuka yayin da yan ta'addan suka farmaki ƙauyen ranar Alhamis, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.
Yace yan bindigan sun shigo da misalin ƙarfe 4:30 na yamma, suka buɗe wa mutanen da ba ruwan su wuta kan mai uwa da wabi, nan take suka kashe mutum huɗu.
Yan bindiga sun tare hanya
Mutumin ya ƙara da cewa a wannan rana ta Alhmis, yan bindigan suka sake kai hari suka toshe hanyar Naka – Makurdi kusa da ƙauyen Ahume da misalin ƙarfe 7:00 na dare.
Tare hanyar ke da wuya, yan bindigan suka buɗe wa matafiya wuta kan mai uwa da wani, yayin haka mutum ɗaya ya rasa rayuwarsa, mutanen da suka mutu suka kai adadin mutum 5.
Tsohon jami'in yaɗa labarai na ƙaramar hukumar Gwer, Francis Ugbede, yace daga cikin waɗan da harin farko ya shafa, har da mahaifi da kuma ɗansa.
Wane mataki hukumomi suka ɗauka?
Shugabar ƙaramar hukumar Gwer West, Mrs Grace Igbabon, ta tabbatar da kai hare-haren ga manema labarai, ta ce ta taimaka wa sojoji da motoci.
The Nation ta rahoto shugabar Ta ce:
"Mun baiwa sojoji kyautar motoci 10 domin su ƙara zage dantse wajen sintiri a yankin."
Yayin da muka tuntuɓi kakakin hukumar yan sanda reshen jihar Benuwai, SP Catherine Anene, ta ce ba ta samu bayanai game da lamarin ba a halin yanzu.
A wani laabarin kuma kun ji cewa Gwamna ya shirya tattaunawa da kungiyoyin dake aikata ta'addanci a jiharsa.
Gwamnatin jihar Oyo ta fara shirin tattaunawa da kungiyoyin da basa ga maciji domin dakile kashe-kashe a faɗin jihar.
Kwamishinan labarai da wuraren buɗe ido, Wasiu Olatunbosun, ya ce bayan haka duk kungiyar da ta cigaba zata ɗanɗana kuɗarta.
Asali: Legit.ng