Kotu ta yanke wa korarrun 'yan sanda 2 hukuncin kisa saboda kama su da laifin fashi da makami

Kotu ta yanke wa korarrun 'yan sanda 2 hukuncin kisa saboda kama su da laifin fashi da makami

  • A ranar Alhamis, Alkali Peter Kekemeke na babbar kotun Abuja ya yanke wa korarrun ‘yan sanda 2 hukuncin kisa bisa kama su da laifin fashi da makami
  • Wadanda aka yanke wa hukuncin sun hada da James Ejah da Simeon Abraham wadanda kwamishinan ‘yan sandan FCT ya gurfanar da su a shekarar 2017
  • Yayin yanke hukuncin, Alkalin ya bayyana yadda aka kama su dumu-dumu da laifukan don har shaidu hudu sai da suka tabbatar da laifukan

FCT, Abuja - Alkali Peter Kekemeke na babbar kotun Abuja ya yanke wa wasu korarrun ‘yan sanda biyu, James Ejah da Simeon Abraham hukuncin kisa a ranar Alhamis, Daily Nigerian ta ruwaito.

Kwamishinan 'yan sandan FCT ne ya gurfanar da su gaban kotun a ranar 20 ga watan Oktoban 2017 bisa zargin su da makirci tare da fashi da makami.

Kara karanta wannan

Ana ta bincike: Hukumar 'yan sanda ta dakatar da 2 daga cikin abokan harkallar Abba Kyari

Kotu ta yanke wa korarrun 'yan sanda 2 hukuncin kisa saboda kama su da laifin fashi da makami
Kotu ta yanke wa korarrun 'yan sanda hukuncin kisa saboda fashi da makami. Hoto: Daily Nigerian
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yayin yanke hukuncin, Kekemeke ya bayyana yadda aka kama korarrun ‘yan sandan dumu-dumu da laifukan bayan shaidu hudu sun bayyana gaban kotu.

Alkalin ya shaida cewa hujjojin da aka gabatar gaban kotu sun nuna cewa tabbas sun yi fashin.

Ya kara da cewa babu wata shaida wacce ta zarce su da suka amsa laifukan su da bakunan su.

Alkali ya ce bai dace wadanda ya kamata su kare jama’a su dinga cutar da su ba

A cewarsa kamar yadda Daily Nigerian ta nuna:

“Abinda ya rage min shi ne in ce ku tafi inda ba za ku sake zunubi ba kamar yadda doka ta tanadar. Doka ta daura nauyi a kai na.
“Yan kasa da dama suna kokawa akan yadda jami’an tsaro musamman ‘yan sanda suke amfani da bindigogi wurin tatsar su. Mutanen da ya kamata su kare su sun koma cutar da su.

Kara karanta wannan

Kamar a jahiliyya: Uba ya kashe 'ya'yansa tagwaye, za a rataye shi har sai ya mutu

“Don haka wajibi ne a yanke muku hukuncin da ya dace da ku don masu fatan yin makamancin halin ku su sauya tunani. Ku ba abin tausayi bane.
“Kamar yadda doka ta tanadar. Na yanke wa mai laifi na farko da na biyu hukuncin kisa.”

Alkali ya nemi a mayar da abubuwan da suka kwata zuwa asusun gwamnati

Ya umarci a mayar da duk abubuwan da suka kwata a hannun jama’a ga gwamnatin tarayya da kuma bangaren yaki da ta’addancin da masu laifin suka yi aiki.

A ranar 20 ga watan Oktoban 2017, lauya mai gabatar da kara, Kufureabasi Ebong ya sanar da kotu yadda suka aikata laifin.

An sha mamaki bayan gano cewa gardin namiji aka tura gidan yari na mata ba tare da an gane a kotu ba

Wani lamari mai ban mamaki ya auku a gidan gyaran halin mata da ke Shurugwu a makon da ya gabata, inda aka gano wata fursuna ba mace bace, katon namiji ne kamar yadda LIB ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Kotu ta sa a yi wa matashin ɗan kasuwa Bulala Bakwai a jihar Kaduna

Praise Mpofu mai shekaru 22 ya na sanye da suturar mata ne a lokacin da aka kama shi inda ya bayyana kamar karuwa don ya yaudari maza ya yi musu sata.

An kama Mpofu ne bayan ya yi wa wani mutum da ke yankin Gweru sata. An samu rahoto akan yadda mutumin ya caskewa Mpofu kudi don su kwana tare da shi a tunanin sa mace ne, daga nan Mpofu ya yashe shi ya tsere.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164