Ahmad Musa ya yiwa tsohon dan kwallon da ya talauce kyautar N2m
- Ahmad Musa ya yiwa daya daga cikin wadanda suka lashe gasar Olympics kyautar milyan biyu
- Dan kwallon wanda ya shahara da yi kyauta da kyautatawa marasa galihu ya sha yabo daga bakin yan Najeriya
- Wannnan ya biyo bayan kyautar kudi da ya bada $1500 don ginin Masallaci a kasar Kamaru
Kyaftin na Super Eagles, Ahmad Musa, ya yiwa tsohon dan kwallon Najeriya a gasar Atlanta ’96, Kingsley Obiekwu, kyautar milyan biyu bayan samun labarin mutumin ya koma direban tasi saboda talauci.
Premium Times tace duk da cewa Musa bai bayyanawa duniya ya yi wannan kyauta ba, ya tabbatar mata lallai haka ne.
Obiekwu kuwa ya tabbatar da samun kyatar kudi daga wajen Musa.
Obiekwu a hirar da yayi da kamfanin dillancin labarai NAN ranar Talata ya bayyana irin halin kuncin da yake ciki.
Yace ya koma amfani da motarsa wajen aikin Tasi ne don ciyar da iyalansa.
Tsohon dan kwallon wanda akafi sani da Shagari a zamaninsa ya ce abubuwa sun tabarbare masa tun lokacin da ya dawo Najeriya a 2008.
A cewarsa, yanzu shine kocin INGAS FC a Enugu, amma yana hada aikin da tukin mota.
A cewarsa:
"Lallai ni direban tasi ne; babu abin boyewa a wurin. Wajibi ne namiji ya nemi halas don ciyar da iyalansa."
"Ina da yara hudu dake jami'ar fasaha ta Enugu kuma dan autana na aji biyar na Firamare."
Ahmed Musa ya gwangwaje Masallacin Garoua da tallafin $1500
A baya kun ji cewa, Ahmed Musa, ya gwangwaje wani masallacin Juma'a da ke Garoua a kasar Kamaru da tallafin $1,500 bayan idar da sallar Juma'a.
Masallacin wanda ya ke kusa da sansanin 'yan wasan kwallon kafa na Najeriya a Garoua, shi ne inda 'yan wasan ke sallah a kowacce rana tun bayan isar su yankin arewacin kasar Kamaru a ranar 5 ga watan Janairu.
Asali: Legit.ng