Jihar Kano ta zo ta biyu cikin jihohin Najeriya 10 da aka fi amfani da yanar gizo, ga jerinsu
Abuja - Hukumar lissafin Najeriya watau NBS ta saki jerin jihohin Najeriya da akafi kira da waya da kuma amfani da yanar gizo a rubu'in karshe na shekarar 2021.
NBS ta bayyana cewa idan aka kwatanta adadin masu kira a waya da amfani da yanar gizo da na shekarar 2020, adadin na 2021 ya ragu.
A jawabin da NBS ta daura a shafinta na yanar gizo, tace:
"A rubu'in karshe na 2021, jimillar mutum 195,463,898 suke kira a waya sabanin rubu'in karshe na 2020 da aka samu mutum 204,601,313."
"Hakazalika mutum 141,971,560 sukayi amfani da yanar gizo."
"Jihar Legas ke kan gaba... biye da jihar Kano da Ogun, yayinda jihar Bayelsa da Ebonyi ne masu mafi karanci."
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ga jerin jihohi 10 da akafi kira a waya da amfani da yanar gizo:
1. Lagos: 18.9m
2. Kano: 9.6m
3. Ogun: 9.1m
4. Oyo: 8m
5. Abuja: 6.9m
6. Kaduna: 6.8m
7. Rivers: 5.7m
8. Delta: 5.3m
9. Edo: 5.2m
10. Niger: 4.9m
5G zai taimaka wajen magance matsalar tsaro a Najeriya, Sheikh Pantami
s da tattalin arzikin zamani, Farfesa Isa Ali Pantami, yace 5G da ake shirin saka wa zai taimaka wajen shawo kan kalubalen tsaro a Najeriya.
Ministan ya yi wannan furuci ne ranar Litinin, a wurin taron gwanjon 3.5 GHz spectrum, wanda hukumar sadarwa ta kasa (NCC) ta shirya a Abuja.
Da yake jawabi a wurin taron kamar yadda The Cable ta rahoto, Pantami ya jaddada cewa sabis ɗin 5G ba shi da wata illa, kuma hukumar lafiya ta duniya (WHO) da kungiyar sadarwa ta ƙasa da ƙasa sun tabbatar da haka.
Asali: Legit.ng