Man Fetur Zai Wadata Zuwa Karshen Wata, Za Mu Raba Lita Biliyan 2, Shugaban NNPC

Man Fetur Zai Wadata Zuwa Karshen Wata, Za Mu Raba Lita Biliyan 2, Shugaban NNPC

  • Babban manajan darekta na NNPC, Mele Kyari ya ce za su tabbatar da yalwatuwar man fetur nan da makwanni kadan
  • A cewarsa, kafin karshen watan nan, za a rarraba lita biliyan 2.1 na man fetur din a cikin kasa don ko wanne yanki ya samu
  • Ya bayar da wannan tabbacin ne yayin taro da kwamitin rikon kwarya ta majalisar wakilai akan binciken mai mara ingancin da aka shigo da shi kasa

FCT, Abuja - Babban manajan darektan hukumar NNPC, Mele Kyari ya ce rarraba man fetur zai tabbata cikin makwanni kadan masu zuwa, Vanguard ta ruwaito.

Manajan ya ce zuwa karshen wannan watan za a rarraba Lita miliyan 2.1 na man fetur don ya yalwatu a kasar nan.

Kara karanta wannan

Wahalar man fetur: N600 ake sayar da litan mai yanzu a Abuja

Man Fetur Zai Wadata Zuwa Karshen Wata, Za Mu Raba Lita Biliyan 2, Shugaban NNPC
Zuwa karshen watan nan za mu rarraba Lita biliyan 2.1 na man fetur, Shugaban NNPC. Hoto: Vanguard
Asali: Twitter

Kyari ya bayar da wannan tabbacin ne yayin wani taro da kwamitin rikon kwarya ta majalisar wakilar wacce take bincike dangane da gurbataccen man fetur din da aka shigo da shi kasar nan kamar yadda Vanguard ta bayyana.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Rashin mai ya janyo 'yan Najeriya sun takura matukar

Idan ba a manta ba, aukuwar lamarin ne ya janyo man fetur ya yi karanci a kasa har ta kai ga 'yan Najeriya suna cika a gidajen man fetur har da masu bacci a cikin gidajen man.

Kamar yadda ya shaida:

"Za a rarraba Lita biliyan 2.1 kafin karshen watan nan. Zai yalwata ta kai ga ko ina ya samu.
"Ina bayar da tabbacin cewa akwai shirin musamman na raba man. Za mu tabbatar hakan ya auku."

Ku saurari karin bayani ...

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

iiq_pixel