Yawancin matasan da suka kammala karatun digiri ba sa iya ayyukan da aka basu, Pantami

Yawancin matasan da suka kammala karatun digiri ba sa iya ayyukan da aka basu, Pantami

  • Dakta Isa Ali Pantami ya yi kira ga matasa su daina zaman jiran neman aikin gwamnati, su tashi tsaye
  • Ministan ya bayyana cewa mafi akasarin matasan da suka kammala karatun digiri basu iya aikin komai ko an basu
  • A karshe ya yi kira ga matasa su rungumi aikin hannu ta yadda zasu iya taimakawa wajen daukan wasu aiki

Katsina - Ministan sadarwa da tattalin arzikin zaman, Dr. Isa Ali Pantami, ya bayyana cewa yawancin matasan da suka kammala karatun digiri ba sa iya ayyukan da aka basu.

Ya yi Alla-wadai da dabi'ar matasan Najeriya na neman aikin gwamnati maimakon sana'a da kasuwanci wanda zai basu daman daukan wasu aiki don rage rashin aikin yi a Najeriya.

Ministan ya bayyana hakan ne yayin jawabi a taron bada kyautar ga zakarun gasar fasaha da ta gudana a jihar Katsina ranar Talata, rahoton Vanguard.

Kara karanta wannan

Borno: Gwamna Zulum na zawarcin likitoci ta hanyar inganta rayuwarsu a jiharsa, zai kara albashinsu

Pantami yace:

"Ba zamu iya alfahari da ilminmu ba sai muna iya samar da dalibai da masu digiri da zasu iya yiwa kasa dukkan abinda take so."
"A yau, mafi akasarin matasanmu bayan sun kammala digiri basu tunanin aikin hannu, kawai aikin gwamnati suke nema."

Pantami
Yawancin matasan da suka kammala karatun digiri ba sa iya ayyukan da aka basu, Pantami Hoto: FMCDE
Asali: Facebook

Babban kalubalenmu ba rashin aikin yi bane

Pantami ya kara da cewa babban kalubalen Najeriya ba rashin aikin yi bane, kawai rashin kwarewar matasan ne.

A cewarsa, akwai ayyuka da yawa amma ko da ka dauki matashi yayi maka aikin zaka tarar bai iya ba.

Yace:

"Akwai ayyuka da yawa a sashen Injiniyanci, ICT, mai da gas, amma yawancin matasanmu idan ka daukesu aiki, zaka tarar ba zasu iya ba. saboda haka kullum yan kasashen waje suke yi mana ayyukan."

Kara karanta wannan

Kisan Hanifa Kano: Matan Arewa sun bukaci gwamnati ta hukunta iyaye saboda abu ɗaya

Ku maida hankali kan Kwarewa fiye da samun takardar Satifiket, Pantami ya shawarci Matasa

Isa Pantami, ya jaddada bukatar gwamnati a kowane mataki da makarantu su fi maida hankali kan kwarewa fiye da samun takardar shaida (Certificate).

Pantami yace hakan ba wai zai samar da ayyukan yi bane kaɗai, zai shawo kan matsalolin zaman kashe wando da kuma magance ƙalubalen da ƙasar nan ke fama da su.

Bayan haka, Farfesa Pantami ya roki waɗan da suka shirya gasa su ɗauki bayanan mutanen da suka fafata domin samun saukin nemo su nan gaba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng