Yanzu-Yanzu: Buhari Ya Naɗa Mohammed Bello Koko a Matsayin Shugaban NPA Mai Cikakken Iko
- Shugaba Buhari ya amince da nadin Mohammed Bello Koko a matsayin shugaban hukumar tashoshin jiragen ruwa ta Najeriya, NPA
- Ma’aikatar sufuri ta sanar da hakan a ranar Talata ta wata takarda wacce darektan yada labaran ma’aikatar, Eric Ojiekwe ya sa hannu
- Kafin a nada shi, Koko ne darektan sha’anonin kudi da gudanarwa na hukumar NPA din, kamar yadda takardar ta bayyana
Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da nadin Mohammed Bello Koko a matsayin shugaban hukumar kula da tashohin jiragen ruwa, NPA, mai cikaken iko, The Cable ta ruwaito.
Mai magana da yawun ma'aikatar sufuri na tarayya, Eric Ojiekwe, ne ya sanar da hakan cikin wata takarda da ya fitar a ranar Talata.
Kafin nadinsa, Koko ne babban direktan sashin kudi da gudanar da mulki a NPA kamar yadda sanarwar ta ce.
Koko zai maye gurbin Hadiza Bala Usman, wacce aka dakatar a watan Mayun 2021 bisa zargin batar da Naira miliyan 165.
An dakatar da Usman ne bayan ministan sufuri, Rotimi Amaechi ya hada wani kwamiti wanda zai yi bincike akan yadda ake gudanar da ayyukan NPA.
Bayan dakatar da ita, Buhari ya nada Koko a matsayin shugaban NPA na wucin-gadi kafin a kammala binciken.
An zargi Usman da wawusar Naira biliyan 165, zargin da ta musanta
A shekarar da ta gabata, The Cable ta ruwaito yadda ministan ya zargi hukumar, karkashin shugabancin Usman da rashin shigar da rarar kudi ta Naira biliyan 165.
Usman ta musanta duk zargin da aka yi mata, sannan ta kalubalanci kowa inda tace a bayyana wata shaidar da zata tabbatar bata shigar da kudin ba.
Sai dai kwamitin bata gano wata shaidar wawusar kudin ba bayan gudanar da binciken.
Gwamna ya kori surukinsa daga aiki, ya umurci kwamishina ya maye gurbinsa
A wani rahoton, Gwamnan Jihar Abia, Okezie Ikpeazu, ya sanar da korar surukinsa, Mataimakin Manajan, Hukumar Kare Muhalli ta JIhar Abia, ASEPA, ta Aba, Rowland Nwakanma, a ranar Alhamis, The Punch ta ruwaito.
A cikin wata takarda da sakataren gwamnatin jihar Abia, Barista Chris Ezem ya fitar, Ikpeazu ya kuma 'sallami dukkan shugabannin hukumar tsaftace muhalli a Aba amma banda na Aba-Owerri Road, Ikot Ekpene da Express.'
Amma gwamnan ya bada umurnin cewa dukkan 'masu shara ba a kore su ba, su cigaba da aikinsu na tsaftacce hanyoyi da tituna a kowanne rana.
Asali: Legit.ng