Buhari ya mika wa majalisa karin kasafin kudi, ciki har da na tallafin man fetur N2.557tr

Buhari ya mika wa majalisa karin kasafin kudi, ciki har da na tallafin man fetur N2.557tr

  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mika wata wasika ga majalisar dokokin kasar nan yau Talata
  • Ya nemi majalisar ta amince da karin kasafin kudin 2021 domin kashe wasu kudade da shugaban ya nema
  • Shugaban majalisar dattawan Najeriya, ya karanta wasikar a gaban majalisa, inji rahotannin da muka samo

FCT, Abuja - Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aika da karin kasafin kudi ga majalisa domin tantancewa da amincewar majalisar dokokin kasar, The Nation ta ruwaito.

Shugaban majalisar dattawa Ahmad Lawan ne ya karanta wasikar da shugaba Buhari ya aiko.

Majalisar dokokin Najeriya
Da dumi-dumi: Shugaba Buhari ya mika wa majalisa karin kasafin kudi | Hoto: dailynigerian.com
Asali: Facebook

Bukatar da Buhari ya mika taba neman karin kudin tallafin man fetur; kudin da ya kai N2.557, inji rahoton Premium Times.

Kasafin kudin inji Buhari na nufin samar da tallafin man fetur daga watan Yuni zuwa Disamba 2022.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Buhari Ya Naɗa Mohammed Bello Koko a Matsayin Shugaban NPA Mai Cikakken Iko

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wannan dai na zuwa ne kimanin wata guda bayan da gwamnatin tarayya ta dakatar da shirinta na cire tallafin man fetur.

Ministar Kudi, Zainab Ahmed, ta ce Naira Biliyan 443 ne kawai aka ware don samar da tallafin mai a 2022.

Ta kuma ce kamfanin man fetur na kasa (NNPC) ya bukaci gwamnatin tarayya da ta samar da jimillar naira tiriliyan 3 domin tallafin mai a 2022.

Hakazalika, shugaban ya nemi a yi kwaskwarima a bangarori da yawa na kasafin kudin na 2022.

Kasafin Kudi: Za'a kashe N35m wajen kwashe Masai a Aso Villa, a 2022

A wani labarin, duk da kudaden da aka kebancewa hukumar EFCC da ICPC, fadar shugaban kasan ta shirya kashe N7.34 million wajen yaki da rashawa a 2022.

Wannan na kunshe cikin daftarin kasafin kudin da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gabatar gaban majalisar dokokin tarayya ranar Alhamis, 7 ga Oktoba, 2021.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Shugaba Buhari zai shilla kasar Belgium halartar wani taro

A lamba ta 22021017, za'a bukaci N7,341,583 donyaki da rashawa a fadar shugaban kasa kadai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.