Karfin hali: EFCC ta kwamushe wani mutum da ke ikirarin shi PA ne na gwamnan jiha
- Hukumar EFCC ta kame wani mutumin da ke shiga rigar mai taimakawa gwamnan jihar Oyo alhali kuma karya yake
- Hakazalika, an kame wasu mutane sama da 20 da ake zargi da aikata laifin sata ta yanar gizo, inji rahoto
- A yanzu dai suna hannun jami'an hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC shiyyar Ibadan a jihar Oyo
Jihar Oyo - Jami’an rundunar EFCC shiyyar Ibadan sun kama wani mutum Babawale Daniel Olayinka, da ke cewa shi “Mai taimaka wa Gwamnan Jihar Oyo, Seyi Makinde kan harkokin yada labarai”.
Hukumar EFCC ta kuma kama wasu mutum ashirin da biyar a unguwar Soka da ke Ibadan, jihar Oyo, bisa zargin zamba ta yanar gizo, Daily Trust ta rahoto.
Da yake gabatar da wanda ake zargin a garin Ibadan, ofishin EFCC, ya ce an karbo katin shaida daga hannun Babawale Daniel Olayinka, daya daga cikin mutane 25 da ake tuhuma da damfarar yanar gizo.
Hukumar ta ce katin shaidan na nuna cewa, shi mataimaki na musamman ne kan harkokin yada labarai ga gwamnan jihar Oyo, Oluseyi Abiodun Makinde.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A cewar mai magana da yawun hukumar ta EFCC, Wilson Nwajuren, kamen ya biyo bayan wasu bayanan sirri da aka samo na aikata laifuka ta yanar gizo.
Ya ce 25 daga cikin wadanda ake zargin sun amince da hannu a ayyukan damfara ta yanar gizo.
Wadanda aka kama
Wadanda ake tuhumar, a cewar sanarwar jaridar Nigerian Tribune tace ta samu sun hada da:
- Wale Jegede
- Adekunle Solomon
- Babawale Daniel Olayinka
- Olanipekun Adams
- Toheeb Ademola
- Olatunji Gbolahan
- Oyowevotu Moses
- Olaide Ibrahim Opeyemi
- Olamilekan Rilwan
- Olamilekan Akinyemi
- Lekan Adenuga
- Salami Segun
- Lawal Samuel
- Kolawole Fuad.
- Olarenwaju Gbolahan
- Makinde Olamposi
- Michael Timileyin
- Sheriff Ololade
- Adewale Dayo
- Ajobola Tajudeen
- Kazeem Warrees
- Obinna Duru
- Shotayo Sola
- Mohammed Suleiman
- Makinde Ajibola
A wani labarin, Rundunar Sojin Najeriya ta tabbatar da tsare wata Soja da ta amince da bukatar auren wani dan bautar kasa a sansanin NYSC da ke Kwara.
Bidiyon masoyan da ke yawo an ga lokacin da suke abubuwan karbar soyayyar juna, lamarin da ya haifar da cin kalamai iri-iri a dandalin sada zumunta.
A wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar soji Onyema Nwachukwu ya aika wa TheCable Lifestyle a ranar Lahadi, ya ce sojar dai ta karya wasu ka’idojin gidan sojoji.
Asali: Legit.ng