Ka tona asirin jami'anka dake taimakawa masu safarar kwaya: IGP ga Buba Marwa
- Shugaban hukumar yan sanda ya bayyana cewa ba jami'ansa kadai suka hada baki da masu safarar kwaya ba
- IGP Alkali ya ce hasali ma jami'an hukumar NDLEA sun karbi cin hanci hannun masu kwayan kuma sun barsu sun wuce
- Ya yi kira ga Janar Buba Marwa ya gudanar da binciken kansa kuma ya damke na hukumarsa inda gaskiya za'a yi
Abuja - Sifeto Janar na yan sanda, IGP Usman Baba Alkali, ya yi kira ga Shugaban hukumar hana fasa kwabrin muggan kwayoyi, Janar Buba Marwa (mrty) ya damke jami'ansa dake taimakawa masu safarar kwaya tare da Abba Kyari.
Shugaban yan sandan ya bayyana hakan ne a jawabin da Kaakin hukumar ya saki ranar Litinin yayinda yake sanar da damke Abba Kyari.
Yace:
"Binciken da yan sanda suka gudanar ya nuna cewa masu safarar kwayoyin na da alaka mai karfi da jam'an NDLEA a tashar jirgin saman Akamu Ibiam dake Enugu saboda suna biyansu kudade."
"Masu safarar kwayoyi biyun da aka kama sun tabbatar da cewa sun dade suna harka tare da jami'an NDLEA tun 2021 kuma a kan lamarin 19 ga Junairu, 2021, an barsu sun wuce da kwayoyin."
Mu muka kama yan kwaya ba NDLEA ba
IGP yace jami'an yan sanda ne suka kamasu ba jami'an NDLEA ba, jami'an NDLEA sun barsu sun wuce saboda an basu cin hanci.
A cewarsa, masu safarar kwayar na turawa jami'an NDLEA hotunansu kafin su isa tashar jirgin sama, saboda haka suna ganinsu suke barinsu su wuce.
Yace:
"Jami'an NDLEA sun barsu sun wuce saboda tun kafin su isa Akanu Ibiam an turo musu hotunansu, yayinda suke kokarin fita daga tashar jirgin da kwayoyi ne yan sanda suka kamasu."
"Saboda haka, Sifeto Janar na yan sanda ya bukaci Shugaban hukumar hana fasa kwabrin kwayoyi ya tabbatar ya damke jami'an hukumarsa dake hada baki da yan kwayan kuma ya gudanar da bincike."
An mika Abba Kyari ga NDLEA bayan kamo shi da abokan harkallarsa
Abba Kyari ya koma hannun hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) bayan kamo shi da yan sanda sukayi.
Da yake magana bayan hukumar ‘yan sanda ta sanar da kama shi, Babafemi ya ce an mika Kyari da wadanda ake zargi da laifin ga NDLEA domin yi masa tambayoyi da kuma ci gaba da bincike da misalin karfe 5 na yamma.
Asali: Legit.ng