An kama wata mabaraciya da kudi har N500,000 da dala 100 a Abuja, an tsare ta

An kama wata mabaraciya da kudi har N500,000 da dala 100 a Abuja, an tsare ta

  • Wata mabaraciya Hadiza Ibrahim ta shiga hannun hukuma a babbar birnin tarayya Abuja
  • An tattaro cewa an damke matar ne bayan an same ta da wasu makudan kudade da suka hada N500,000 da kuma kudin Amurka dala 100
  • Kakakin hukumar kula da harkoki, zamantakewa da ci gaban babban birnin tarayya, Shaka Sunday, ya ce har yanzu matar bata bayar da wani gamsasshen bayani ba

Abuja - Rahotanni sun kawo cewa an kwamushe wata mabaraciya mai suna Hadiza Ibrahim a Abuja dauke da kudi N500,000 da kuma dala 100.

Jaridar Punch ta rahoto cewa mazauna yankin sun shiga rudani bayan da aka samu matar dauke da wadannan makudan kudade.

An kama wata mabaraciya da kudi har N500,000 da dala 100 a Abuja, an tsare ta
An kama wata mabaraciya da kudi har N500,000 da dala 100 a Abuja, an tsare ta Hoto: Punch
Asali: UGC

Kakakin hukumar kula da harkoki, zamantakewa da ci gaban babban birnin tarayya, Shaka Sunday, ya tabbatar da cewar matar na tsare a hannun hukumar a yankin Bwari.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: An mika Abba Kyari ga NDLEA bayan kamo shi da abokan harkallarsa

Ya bayyana cewa har yanzu wacce ake zargin bata yi bayanin yadda aka yi ta samu makudan kudaden da aka samu a jikinta ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Punch ta nakalto Sunday yana cewa:

“Mun kama wata mata da kudi dala 100 da kuma N500,000.
“Har yanzu matar na cibiyarmu da ke Bwari. Tana karkashin bincike saboda bata bamu cikakken bayani mai amfani da kuma yadda ta samu kudin ba.”

Duniya kenan: Mai shekaru 16 ya saci yarinya 'yar shekaru 4, ya nemi fansan N70,000 a Katsina

A wani labari na daban, mun ji cewa wata mata da ke wucewa ta wani kango a garin Marabar Kankara da ke karamar hukumar Malumfashi ta jihar Katsina ta ceto yarinya yar shekara hudu da aka yi garkuwa da ita, lamarin da ya taimaka wajen kama wanda ya sace ta.

Kara karanta wannan

Cikakken bayani: 'Yan sanda sun bi Abba Kyari da wasu mutane, sun kwamushe su

A bisa ga rahoton yan sanda, matar wacce ke sane da batun batar yarinyar mai shekaru hudu, tana wucewa ta wani kango a yankin, sai ta hango yarinyar tare da wani Abubakar Abdulbasir.

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa wanda ake zargin, Abubakar Abdulbasir mai shekaru 16 yana a aji uku na karamar sakandare ne a garin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng