Kano: An kama mutum 5 kan zargin kashe wata matar aure a gidanta

Kano: An kama mutum 5 kan zargin kashe wata matar aure a gidanta

  • Yan sanda a Kano sun kama wasu mutane biyar da ake zargi sun kashe wata matar aure a gidanta a karamar hukumar Kumbotso
  • An halaka matar auren, Rukaya, mai shekaru 24 a gidan mijinta a ranar Asabar sannan maharan suka yi wa yaranta duka
  • Mai magana da yawun yan sandan Kano, SP Abdullahi Haruna ya tabbatar da hakan inda ya ce wadanda ake zargin na hannun yan sanda

Jihar Kano - A kama a kalla mutane biyar kan zarginsu da hannu a kisar wata matar aure, mahaifiyar yara biyu, Rukaya Mustapha a Kano.

Vanguard ta rahoto cewa an kashe Rukaya, mai shekaru 24 ne a ranar Asabar a gidan mijinta da ke garin Danbare a karamar hukumar Kumbotso ta Jihar Kano.

Kano: An kama mutum 5 kan zargin kashe wata matar aure a gidanta
An kama mutum 5 kan zargin kashe wata matar aure a Kano. Hoto: The Nation
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun shafe tsawon kwanai 3 suna kai mamaya garuruwan wata jiha a arewa

An kuma gano cewa wadanda ake zargi da kisar ba su bar yaran marigayiyan (Rukaya) ba inda suma suka lakada musu duka.

Yan sanda sun tabbatar da kamen

Mai magana da yawun yan sandan Kano, SP Abdullahi Haruna ya tabbatar da hakan inda ya ce wadanda ake zargin na hannun yan sanda, rahoton Vanguard.

Su kuma yaran marigayiyan, a halin yanzu suna asibiti da ba a bayyana sunansa ba inda suke samun kulawa.

'Yan sanda sun damke ma'aikacin banki da ya kwashewa kwastoma N10m daga asusunsa

A wani labarin daban, Hukumar ‘yan sandan jihar Oyo sun kama wani Adeyemi Tosin, mai shekaru 36, wanda ma’aikacin banki ne bisa zarginsa da kwasar naira miliyan 10 daga asusun wani abokin huldar bankin, Oladele Adida Quadri.

Kakakin hukumar, DSP Adewale Osifeso, ya bayyana hakan a wata takarda a ranar Talata, 17 ga watan Augusta, inda yace Tosin ya saci kudin Quadri, mai shekaru 78 ne da sunan zai taimake shi a reshen bankin na Ibadan bisa matsalar da ya samu wurin cirar kudi a ranar 12 zuwa ranar 13 ga watan Augusta.

Binciken ‘yan sandan ya haifi da mai ido sakamakon umarnin kwamishinan ‘yansandan jihar, Ngozi Onadeko, wacce tasa a yi bincike na musamman.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164