NDLEA sun yi kokari, abin a yaba: Kungiya ta fadi me ya kamata a yiwa Abba Kyari
- Kungiyar kare hakkin bil-adama ta HURIWA ta nemi a kama Abba Kyari, a mika shi ga hukumar NDLEA
- Wannan na zuwa ne bayan da NDLEA ta yada wani bidiyo, inda aka ga Kyari na kokarin kulla harkallar kwayoyi da jami'an NDLEA
- A cewar HURIWA, yanzu dai hujjoji sun tabbata cewa Kyari yana kulla harkalla da mutane don cimma burinsa
Abuja - Kungiyar kare hakkin bil adama ta Human Rights Writers Association of Nigeria (HURIWA), a ranar Litinin, ta yabawa hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa bisa yadda ta fifita aiki fiye da son rai da kishin aljihu.
Kungiyar ta yabawa NDLEA karkashin jagorancin shugabanta Buba Marwa, saboda ayyana neman DCP Abba Kyari, bisa zargin alaka da safarar miyagun kwayoyi, Punch ta ruwaito.
A yau ne sanarwa ta iso Legit.ng Hausa cewa, NDLEA ta ayyana neman Abba Kyari bisa zarginsa da kokarin kulla harkallar safarar miyagun kwayoyi.
Dama dai Kyari na fuskantar tuhume-tuhumen da suka shafi damfarar kudade tare da wani Hushpuppi a kasar Amurka.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A wata sanarwa da babban kodinetan hukumar HURIWA na kasa, Emmanuel Onwubiko ya fitar, ya kuma yi kira ga babban sufeton ‘yan sandan Najeriya, Baba Usman da ya daina baiwa Kyari kariya tare da kama shi cikin gaggawa.
Bukatar HURIWA
Da yake tsokaci game da tuhume-tuhume da Kyari ke fuskanta, kodinetan hukumar ta HURIWA na kasa, Emmanuel Onwubiko, ya ce:
“Yanzu da hukumar NDLEA ta ayyana neman Kyari bisa laifin safarar miyagun kwayoyi, ga kuma kwararan hujjoji da ba za a iya karyatawa ba kamar yadda kafar ta doka ta bayyana, IGP ba shi da wani uzuri sai dai kawai ya gaggauta kama dan sanda don mika shi ga NDLEA.
Hakazalika, kungiyar ta bayyana cewa, komai ma idan akwai shi a rufe to yanzu dai ya bayyana, kuma ya kamata IGP ya yi abin da ya dace.
Sanarwar ta kara cewa, ya zama dole hukumar 'yan sanda ta kori Abba Kyari daga aiki kasancewarsa baragurbi, a cewarta:
“Har ila yau, dole ne hukumar ‘yan sanda ta yi gaggawar korar Kyari daga aikin ‘yan sandan Najeriya."
NDLEA ta gano DCP Abba Kyari na safarar kwayoyi tsakanin kasashe
A tun farko, Hukumar NDLEA ta ayyana jami'in dan sanda shugaban rundunar IRT da aka dakatar, DCP Abba Kyari cikin wadanda take nema ruwa a jallo bisa zargin safarar miyagun kwayoyi.
Hukumar ta NDLEA ta ce bincike ya nuna cewa jami'an da ya shahara kuma yake karkashin bincike bisa zargin hannu a wata damfara, Kyari mamba ne na wata kungiyar harkallar miyagun kwayoyi da ke hada-hadarta a fadin duniya.
Kakakin hukumar ya bayyana haka ne a wata zantawa da manema labarai a ranar Litinin, kamar yadda Legit.ng Hausa ta samo daga NDLEA.
Asali: Legit.ng