Yan bindiga sun yi awon gaba da mata, da 'ya'yan babban jami'in gwamnatin Matawalle a Zamfara
- Yan ta'adda sun saka yankin rukunin gidajen Damba Housing Estate, dake Gusau, a gaba sun kai hari sau uku kenan cikin wata ɗaya
- A daren jiya, wasu yan bindiga da su kai nufin sace Daraktan kuɗi na jihar Zamfara, sun yi awon gaba da iyalansa, matarsa da yayansa biyu
- Yan Bijilanti sun yi kokarin dakile harin amma yan ta'addan suka ci ƙarfin su, suka ji wa mutum biyu raunuka
Zamfara - Yan ta'adda sun farmaki rukunin gidajen Damba Housing Estate, dake Gusau babban birnin jihar Zamfara ranar Lahadi da daddare.
Punch ta tattaro cewa yan bindigan sun yi awon gaba da mata da ƴaƴan Daraktan kuɗi na ma'aikatar kuɗi ta jihar Zamfara, Sirajo Hassan.
Yan ta'addan sun kutsa gidan Daraktan da misalin ƙarfe 1:00 na dare ranar Litinin, da nufin sace shi, amma sai suka taki rashin sa'a bai kwana gida ba.
Yayin da suka tabbatar wanda suka zo nema bayan nan, sai suka iza ƙeyar matarsa, Maryam Gidado, da kuma yaranta biyu, zuwa wani wuri da ba'a sani ba.
Yan Bijilanti sun kai ɗauki
An jiyo ƙarar harbe-harben bindiga yayin da Yan Bijilanti suka gwabza da yan ta'addan a kokarin dakile harin, amma yan ta'addan suka ci ƙarfin su.
Mutum biyu daga cikin Yan Bijilantin sun ji raunuka sanadiyyar harbin bindiga, amma an yi gaggawar kai su Asibiti domin samun kulawar lafiya.
Mazauna yankin rukunin gidajen na rayuwa cikin tsoro da fargaba saboda yawaitar harin yan ta'adda, inda suka yi kira ga jami'an tsaro su agaza musu.
Rahotanni sun bayyana cewa yan ta'adda sun kai hari yankin karo na uku kenan zuwa yanzun cikin wata ɗaya, sun sace akalla mutum tara.
Hukumar yan sanda reshen jihar Zamfara, karkashin jagorancin Kwamishina, Ayuba Elkana, ta ziyarci yankin makon da ya gabata, kuma ya yi alƙawarin tura yan sanda, amma har yau shiru.
A wani labarin kuma kungiyar malaman jami'o'i ASUU ta ayyana ɗaga Pantami zuwa matsayin Farfesa da saɓa wa doka da yi mata karan tsaye
Shugaban ƙungiyar, Farfesa Emmanuel Osodeke, shi ne ya bayyana haka, yace sun ɗauki matakin hukunta jami'ar FUTO.
Ya ce ba zai yuwu ministan a haɗa ayyuka biyu na gwamnatin tarayya a lokaci ɗaya ba, dan haka ta soke matsayin Farfesa da aka ba shi.
Asali: Legit.ng