Da Dumi-Dumi: Ma'aikacin FG ya tsare matarsa da 'ya'yansa da Bindiga, yace sai an biya shi kuɗin da ya kashe

Da Dumi-Dumi: Ma'aikacin FG ya tsare matarsa da 'ya'yansa da Bindiga, yace sai an biya shi kuɗin da ya kashe

  • Wani mutumi ma'aikacin gwamnatin tarayya ya yi garkuwa da matarsa da yayansa, ya nemi a biya shi kuɗin da ya kashe kan su
  • Rahotonni sun bayyana cewa, Mista Felix Akeze, na aiki da hukumar FIRS, kuma ya tsare iyalansa a gida tsawon kwana biyar a Legas
  • A halin yanzun jami'an tsaro sun samu nasarar kubutar da mutanen daga hannunsa, bayan samun rahoto yau da safe

Lagos - Wani Mutumi, Felix Akeze, ma'aikacin hukumar tattara haraji ta ƙasa (FIRS) ya tsare matarsa da kuma yayansa da bindiga da nufin garkuwa a gidansa dake Chevron Drive, Lekki, jihar Legas.

Vamguard ta rahoto cewa Matar da abun ya shafa yar asalin ƙaramar hukumar Igbo Etiti, jihar Enugu, ita ta sanar da ɗan uwanta halin da suke ciki da safiyar yau.

Kara karanta wannan

Sokoto: Iyalan Ma'aikacin gwamnati da aka gano da hannu a ayyukan ta'addanci sun yi magana

Anguwar Lekki a jahar Legas
Da Dumi-Dumi: Ma'aikacin FG ya tsare matarsa da 'ya'yansa da Bindiga, yace sai an biya shi kuɗin da ya kashe Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Matar ta sanar masa da cewa Maigidanta ya bukaci ta biya baki ɗaya kuɗin da ya kashe a kanta da kuma 'ya'yan da suka haifa ko kuma ya kashe su baki ɗaya.

Wane mataki jami'an tsaro suka ɗauka?

Rahotanni sun bayyana cewa jami'an tsaron dake zaune a rukunin gidajen, wanda suka isa kofar gidan tare da yan sanda sun yi matuƙar kokari wajen samun damar shiga harabar gidan.

Jami'an tsaron da kuma yan sanda sun samu nasarar kutsa wa cikin gidan kuma suka ceto matar da kuma ƴaƴanta daga hannun mutumin.

Bayan kubutar da waɗanda abin ya shafa, matar mutumin ta bayyana cewa sun kwashe kwanaki biyar a tsare a hannun maigidanta kuma uban ƴaƴanta.

Matar ta ce:

"Kwana biyar kenan yana tsare da mu, ya bukaci mu biya kuɗin duk da ya kashe a kan mu ko kuma ya kashe mu."

Kara karanta wannan

Sokoto: Kansila ya gwangwaje 'yan unguwarsa da kyautar tabarmai 2, ya jawo cece-kuce

A wani labarin na daban kuma An shiga tashin hankali yayin da tsohon Sarki Sanusi II ya shirya kai ziyara jihar Kano

Manyan masu ruwa da tsaki da masanan tsaro sun bayyana damuwarsu game da jita-jitar tsohon Sarki zai kai ziyara jihar Kano.

Gwamnatin jihar ta bayyana cewa a halin yanzun ba ta da masaniya kan lamarin, idan ma dagaske ne ta na maraba da zuwansa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Tags: