Da Dumi-Dumi: ASUU tace Pantami bai cancanci zama Farfesa ba, zata hukunta FUTO
- Kungiyar Malaman Jami'o'i ta ƙasa (ASUU) ta bayyana ɗaga Minista Pantami zuwa matsayin Farfesa da ƙarya doka
- Shugaban ƙungiyar, Farfesa Emmanuel Osodeke, shi ne ya bayyana haka. yace sun ɗauki matakin hukunta jami'ar FUTO
- Ya ce ba zai yuwu ministan a haɗa ayyuka biyu na gwamnatin tarayya a lokaci ɗaya ba, dan haka ta soke matsayin Farfesa da aka ba shi
Abuja - Ƙungiyar malaman jami'o'i ASUU ta yi watsi da matsayin Farfesa da aka bai wa ministan harkokin sadarwa da tattalin arziƙin zamani, Dakta Isa Pantami.
Punch ta rahoto cewa ƙungiyar bayan taron mambobin majalisar zartarwan ta da ya gudana yau, ta bayyana baiwa Pantami Farfesa a matsayin, "karan tsaye ga doka."
Shugaban ASUU na ƙasa, Farfesa, Emmanuel Osodeke, shi ne ya bayyana haka a wurin taron manema labarai da ƙungiyar ta kira ranar Litinin.
Daily Trust ta rahoto Shugaban ASUU ya ce:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Ba zai yuwu ka zama minista kuma kana koyarwa a jami'a lokaci ɗaya ba. Hakan karfafa guiwa ne a saɓa doka."
"Ya kamata Isa Pantami ya aje mukamin minista ko kuma yunkurin haɗa ayyuka biyu a gwamnatin tarayya. Kwata-kwata bai cancanta ba, dan haka ba za'a ɗauke shi a matsayin Farfesa ba."
"Mun cimma matsayar hukunta mambobin ASUU da ke da hannu a ƙarin matsayin Pantami da kuma mataimakin shugaban jami'ar FUTO (VC)."
ASUU ta tsunduma yajin aiki
Kazalika a yau kungiyar ASUU ta bayyana shiga yajin aikin mako huɗu domin gargaɗi da gwamnatin tarayya kan alƙawurran da ta ɗauka kuma ta gaza cika mata.
Mambobin majalisar zartarwan ASUU sun ɗauki wannan matakin ne bayan ganawar sirri da wakilan ma'aikatar ƙadugo da samar da ayyukan yi da safiyar Litinin, 14 ga watan Fabrairu, 2022.
A wani labarin kuma An shiga tashin hankali yayin da tsohon Sarki Sanusi II ya shirya kai ziyara jihar Kano
Manyan masu ruwa da tsaki da masanan tsaro sun bayyana damuwarsu game da jita-jitar tsohon Sarki zai kai ziyara jihar Kano.
Gwamnatin jihar ta bayyana cewa a halin yanzun ba ta da masaniya kan lamarin, idan ma dagaske ne ta na maraba da zuwansa.
Asali: Legit.ng