Nasara daga Allah: An kashe yan ta’adda da dama yayin da sojoji suka farmaki mafakarsu a Yobe

Nasara daga Allah: An kashe yan ta’adda da dama yayin da sojoji suka farmaki mafakarsu a Yobe

  • Dakarun rundunar sojojin Najeriya sun yi gagarumin nasara a kan yan ta’adda a karamar hukumar Gujba ta jihar Yobe
  • Sojojin sun farmakin mafakar yan ta'addan ne bayan sun samu bayanai a kan shige da ficensu
  • Rundunar sojin sama da na kasa ne suka kai harin a wurare daban-daban na miyagun

Yobe - Rahotanni sun kawo cewa dakarun rundunar sojojin Najeriya sun kashe yan ta’adda da dama a karamar hukumar Gujba ta jihar Yobe.

Jaridar The Cable ta rahoto daga majiya cewa dakarun sun aiwatar da wani aikin mamaya biyo bayan bayanai da suka samu kan shige da ficen yan ta’addan a daren ranar Juma’a, 11 ga watan Fabrairu.

Nasara daga Allah: An kashe yan ta’adda da dama yayin da sojoji suka farmaki mafakarsu a Yobe
Sojoji sun kashe yan ta’adda da dama yayin da suka farmaki mafakarsu a Yobe Hoto: HQ Nigerian Army
Asali: UGC

Dakarun rundunar sojin sama na Najeriya da na kasa ne suka aiwatar da aikin tsaron.

Kara karanta wannan

'Karin bayani: An ji harbe-harben bindiga yayin da rikici ya ɓarke tsakanin mambobin NURTW

An tattaro cewa yan ta’addan sun doshi kauyukan Talala, Mungusum, Abbah Bakari da Buk a yankin Damboa, yayin da aka ce an gano wasun su a kewayen tsaunin Ngulde kusa da Chibok.

Har wayau, an gano wasu a kusa da sansanonin tsaunin Mandara, Gargash, Izza, Bula Bakakai da Gobara.

Rahoton ya ce yan ta’addan na kokarin tserewa garuruwa a jumhuriyyar Nijar tare da wasu mutane da ake zaton iyalansu ne.

The military operation is part of efforts by the Nigerian Army, under operation Sahel Sanity, to address insecurity in communities in the north and along the Lake Chad axis.

Aikin sojojin na daga cikin kokarin da rundunar sojin Najeriya karkashin atisayen operation Sahel Sanity ke yi domin magance matsalar rashin tsaro a garuruwan da ke arewa da kuma yankin tafkin Chadi.

Kara karanta wannan

Nasara: Jiragen yakin Najeriya sun kashe shugabannin yan bindiga da yaransu 37 a Neja

Nasara daga Allah: Sojoji sun kashe 'yan ISWAP da B/H 120, sun kamo 50, sun kwato makamai

A wani labarin, mun kawo a baya cewa, dakarun rundunar sojojin Najeriya karkashin atisayen Operation HADIN KAI sun kashe mayaka 120 a cikin yan makonnin da suka gabata.

Daraktan yada labarai na ayyukan tsaro, Manjo Janar Bernard Onyeuko ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis, 10 ga watan Fabrairu, a taron manema labarai wanda wakilin Legit.ng ya halarta a Abuja.

Ya ce dakarun sun kuma kama yan ta’adda 50, sannan suka kwato motocin harbi guda 5, makamai iri-iri guda 50 da kuma alburasai daban-daban guda 200 daga yan ta’addan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng