Muhimman abubuwa 5 game da rayuwar Magajin Garin Sokoto, Hassan Ahmad Danbaba

Muhimman abubuwa 5 game da rayuwar Magajin Garin Sokoto, Hassan Ahmad Danbaba

A yau Asabar 12 ga watan Fabrairu ne Magajin Garin Sokoto, Alhaji Hassan Ahmad Danbaba ya riga mu gidan gaskiya.

Ya rasu ne bayan gajeruwar rashin lafiya a garin Kaduna kamar yadda majiya na kusa da iyalansa ta bayyana.

Muhimman abubuwa 5 game da rayuwar Magajin Garin Sokoto, Hassan Ahmad Danbaba
Hassan Ahmad Danbaba: Muhimman abubuwa 5 game da rayuwar Magajin Garin Sokoto. Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Ga wasu muhimman abubuwan biyar da ya kamata a sani game da marigayin;

1. Alhaji Hassan Ahmad Danbaba jika ne ga marigayi Firimiya Arewa, Sir Ahmadu Bello Sardaunan Sokoto.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

2. Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta nada shi a matsayin shugaban wucin gadi a Hukumar Kula Da Albarkatun Ruwa na Sokoto-Rima a shekarar 2020.

Kara karanta wannan

Sarkin Musulmi, El-Rufai Da Wasu Gwamnoni Biyu Sun Hallarci Jana’izar Jikan Sardauna Da Aka Yi a Sokoto

3. Ya shafe shekaru 25 a kan kujerar mulki ta Magajin Garin Sokoto.

4. Mahaifiyarsa, Hajiya Aishatu ce babban 'yar marigayi Firimiyan Arewa, Sir Ahmadu Bello Sardaunan Sokoto.

5. An samu rashin jituwa tsakaninsa da Sarkin Musulmi, Alhaji Sa'ad Abubakar, kan wata bincike da aka ce EFCC ta yi.

Sarkin Musulmi, El-Rufai Da Wasu Gwamnoni Biyu Sun Hallarci Jana’izar Jikan Sardauna Da Aka Yi a Sokoto

A wani labarin, Sarkin Musulmi, Muhammad Abubakar, tare da Gwamna Nasir El-Rufai na Jihar Kaduna, Aminu Tambuwal a Jihar Sokoto tare da Atiku Bagudu na Jihar Kebbi suna cikin manyan mutanen da suka halarci jana’izar jikan Sardaunan Sokoto, Hassan Danbaba, a ranar Asabar a garin Sokoto.

Babban limamin masallacin Sultan Bello, Muhammad Akwara, ya ce ko wanne mai rai mamaci ne don haka ya bukaci mutane su kasance masu bin dokokin Allah yayin da suke da rai, Premium Times ta ruwaito.

Kara karanta wannan

'Karin Bayani: Yadda Jikan Sardauna, Magajin Garin Sokoto, Hassan Danbaba, Ya Rasu

An birne Danbaba kamar yadda dokar musulunci ta tanadar a Binaci, kusa da fadar Sultan, makabartar iyalan Magajin Gari.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164