Shugaba Buhari ya kori hadimar Aisha Buhari, Zainab Kazeem

Shugaba Buhari ya kori hadimar Aisha Buhari, Zainab Kazeem

  • Shugaba Muhammadu Buhari ya sallami hadimar Asiha Buhari, Zainab Kazeem, mataimakiya na musamman ga shugaban kasa bangaren ayyukan gida da taruruka, daga aiki
  • Buhari ya kuma amince da nadin Muhammad Sani Zorro, dan jarida, dan siyasa kuma tsohon dan majalisa a matsayin hadimin shugaban kasa a bangaren harka da al'umma da tsare-tsare, a ofishin First Lady
  • An kuma yi wa wasu mutane uku canjin wurin aiki, sune Dr Muhammad Kamal Abdulrahman, Hadi Uba, da Wole Aboderin

Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da nadin Muhammad Sani Zorro, dan jarida, dan siyasa kuma tsohon dan majalisa a matsayin babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa a bangaren harka da al'umma da tsare-tsare, a ofishin First Lady.

Shugaba Buhari ya kori hadimar Aisha Buhari, Zainab Kazeem
Shugaba Buhari ya kori hadimar Aisha Buhari. Hoto: Vanguard
Asali: Twitter

Kara karanta wannan

2023: Tinubu ya naɗa ɗan shekaru 31 a matsayin shugaban watsa labaransa na ƙasa

Shugaban kasar ya kuma amince da korar Zainab Kazeem, mataimakiya na musamman ga shugaban kasa bangaren ayyukan gida da taruruka, ofishin First Lady.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sabon nadin da korar na cikin wata sanarwa ce ta babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa a bangaren jarida da watsa labarai, Mallam Garba Shehu ya fitar a shafinsa na Twitter.

Wadanda aka sauya wa wurin aiki

Sanarwar ta kuma yi bayanin cewa bisa bukatar na First Lady, Mrs Aisha Muhammadu Buhari, "Shugaban kasar ya amince da sauya wa wasu masu rike da mukaman siyasa wurin aiki daga ofishinta zuwa ofishin sakataren gwamnatin tarayya, kafin a tura su wasu hukumomin ko ma'aikatu."

Wadanda canjin wurin aikin ya shafa sune: Dr Muhammad Kamal Abdulrahman, Babban Mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan lafiya da abokin huldar cigaba kuma likitan First Lady; Hadi Uba, Mataimaki na musamman ga Shugaban Kasa kan mulki da Wole Aboderin, Mataimaki na musamman ga Shugaban kasa kan Kungiyoyi masu zaman kansu, NGOs.

Kara karanta wannan

Fadar Shugaban kasa: Buhari ya yi ganarwar sirri da TY Danjuma da Mohammed Indimi

Sanarwar ta kuma ce:

"Daga ranar 11 ga watan Fabrairu an kore Zainab Kazeem, Mataimakiya na musamman ga shugaban kasa a ayyukan gida da taruruka, ofishin First Lady daga aiki."

Mukamman da Zorro ya rike

A cewar sanarwar, Zorro, shahararren dan jarida zai kawo kwarewarsa da bangaren jarida, wallafa labarai da jagoranci ga aikin.

"A lokuta da dama, ya rike mukamin shugaban kungiyar yan jarida ta Najeriya, NUJ, Kungiyar yan jarida na Afirka ta Yamma, WAJA, da Kungiyar yan jarida ta Afirka, FAJ.
"Ya kuma rike mukamin shugaban kwamitin 'yan gudun hijira, wadanda suka rasa muhallinsu a Arewa maso Gabas."

Gwamna ya kori surukinsa daga aiki, ya umurci kwamishina ya maye gurbinsa

A wani labarin, Gwamnan Jihar Abia, Okezie Ikpeazu, ya sanar da korar surukinsa, Mataimakin Manajan, Hukumar Kare Muhalli ta JIhar Abia, ASEPA, ta Aba, Rowland Nwakanma, a ranar Alhamis, The Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: Mun fara shawara kan mikawa gwamnatin Amurka Abba Kyari

A cikin wata takarda da sakataren gwamnatin jihar Abia, Barista Chris Ezem ya fitar, Ikpeazu ya kuma 'sallami dukkan shugabannin hukumar tsaftace muhalli a Aba amma banda na Aba-Owerri Road, Ikot Ekpene da Express.'

Amma gwamnan ya bada umurnin cewa dukkan 'masu shara ba a kore su ba, su cigaba da aikinsu na tsaftacce hanyoyi da tituna a kowanne rana.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164