Kai tsaye: Yadda zaben kananan hukumomin Abuja 6 ke gudana yau Asabar
A yau, 12 ga watan Febrairu 2022, za'a gudanar da zaben kananan hukumomin birnin tarayya Abuja shida.
Sabanin sauran jihohin Najeriya, hukumar INEC da kanta ke gudanar da zaben Abuja.
A bisa alkaluman INEC, mutum 55 ke neman kujeran shugabannin kananan hukumomi yayinda mutumin 363 ke neman kujerar Kansila
Kananan hukumomin sune:
1. Abuja Municipal (Cikin gari)
2. Bwari
3. Kwali
4. Gwagwalada
5. Kuje
6. Abaji
Ka jerin yan takaran:
Na'urar BVAS na aiki yadda ya kamata a Bwari yayinda wasu ke korafi a wasu wurare
An fara zabe a Gwagwalada Abuja
Dattijo ya kada kuriarsa a Gwarimpa
An fara zabe a Bwari Central
Mutane da dama sun fito kada kuri'arsu
An fara zabe a sassan Abuja
AMAC
Akwatin zaben Suncity Estate, AMAC
An fara tantance masu zabe kuma mutumin farko ya kada kuri'arsa. Mutanen da ke nan kalilan ne.
Kuje
An fara tantance masu zabe a fadar Sarki kusa da kasuwar Amebo, Pasali,Kuje.
Amsco Estate Galadimawa
Jami'an INEC sun isa wajen amma babu mutum ko guda da yazo kada kuri'a. Duka-duka mutum 5 akayi rijista a akwatin.
PU 014 Gwarimpa Ward
A makarantar Firamaren Jabi Sariki, an fara tantance masu zabe kuma sun fara kada kuri'unsu.