Yanzu-yanzu: Yan bindiga sun kashe Diraktan ayyukan hukumar KADGIS a gidansa
- An hallaka diraktan ma'aikatar KADGIS na jihar Kaduna cikin gidansa ranar Talata cikin dare
- An tattaro cewa shi kadai aka kashe a gidan kuma basu saci komai ko kowa ba
- Hukumar yan sandan jihar da Gwamnatin jihar har yanzu basu yi tsokaci kan lamarin ba
Kaduna - Yan bindiga kimanin mutum biyar cikin daren Juma'a sun hallaka Diraktan ayyuka na hukumar bayanan jihar Kaduna KADGIS, Alhaji Dauda Anchau, a gidansa.
Daily Trust ta ruwaito cewa yan bindigan sun dira gidansa ne dake unguwar Barakallahu, karamar hukumar Igabi inda suka hallakashi.
An tattaro cewa yan bindigan basu dauki komai a gidan ba, kawai kasheshi suka yi suka tafi.
Dagacin garin, Alhaji Muhammad Abdullahi, ya tabbatar da labarin harin inda yace DPOn yan sandan unguwar Rigachukuwun da Barnawa sun ziyarci wajen.
A cewarsa:
"Wannan kisan kai ne kawai saboda gidansa suka je, suka kashe shi kuma basu dauki komai a gidanba kuma basu taba maigadinsa da matarsa ba."
"Ko daya kauyen da suka kai hari, ba'a kashe kowa ba, kawai sun taba kura ne suka tafi. Sun yi hakan ne don ayi tunanin unguwar suka kai hari."
Yan bindiga sun kaiwa tsohon Soja AVM Maisaka hari gidansa dake Rigasa
Haka wasu tsagerun yan bindiga suka hallaka wani tsohon Sojan sama, Air Vice Marshal, Mohammed Maisaka, a gidansa dake unguwar Rigasa a jihar Kaduna.
Rahoton Daily Trust ya nuna cewa yan bindiga sun bindigeshi tare da jikansa, Mohammed Musa, wanda shima Soja ne.
Wani mazaunin unguwar da Legit Hausa ta tuntuba ya bayyana cewa dogarinsa ne aka kashe ba jikansa ba.
An tattaro cewa yan bindigan sun dira gidan da daren Litnin misalin karfe 8:30 na dare kuma suka harbesu har lahira.
Asali: Legit.ng