Batanci ga annabi: Kotu ta dage zaman Sharrif-Aminu da watanni 2

Batanci ga annabi: Kotu ta dage zaman Sharrif-Aminu da watanni 2

  • Matashin da aka yankewa hukuncin kisa kan batanci ga Annabi, Sharif-Aminu na cigaba da gurfana a kotu
  • Sharif-Aminu ya bukaci kotun tayi watsi da dokar shari'ar Musulunci saboda ta sabawa kundin tsarin mulkin Najeriya
  • Kotu ta sake dage zaman da watanni biyu saboda gwamnatin Kano ta yi jinkirin martani kan bukatar Sharif-Aminu

Kano - Kotun daukaka kara dake jihar Kano ta dage zaman Yahaya Sharif-Aminu wanda akewa zargin wakar batanci ga Annabi (SAW) kuma aka yankewa hukuncin kisa.

An dage zaman ne saboda gwamnatin Kano a ranar Alhamis ta bukaci a kara mata lokaci don martani kan bukatar lauyoyin Sharif-Aminu.

Batanci ga annabi: Kotu ta dage zaman Sharrif-Aminu da watanni 2
Batanci ga annabi: Kotu ta dage zaman Sharrif-Aminu da watanni 2
Asali: Facebook

Kara karanta wannan

An garkame dan majalisar wakilan tarayya kan almundahanar N185m

Yayinda aka dira kotu ranar Alhamis, lauyan Sharif, Kola Alapini ya shirya yiwa Alkali maganar ayi watsi da karar.

Kawai sai lauyan gwamnati, Sani Ahmed, ya bayyana inda ya bukaci kotu ta karawa gwamnatin jihar lokaci don martani kan bukatar Yahaya Sharif.

Kwamitin Alkalan karkashin jagorancin Mai shari'a, George Mbaba, ya dage zaman zuwa ranar 12 ga Mayu, 2022.

Sharif-Aminu ya bukaci kotu tayi watsi da karar da aka shigar kansa

Yahaya Sharif-Aminu,ya bukaci kotun daukaka kara ta hana sake gurfanar da shi kan laifin batanci.

Lauyan Sharin Aminu ya bukaci kotun daukaka karar tayi watsi da shari'ar babbar kotun jihar ta da tace a sake gurfanar da shi. Yace kawai yanzu a wankesa daga laifin kuma a sakesa.

Hakazalika ya yi kira ga kotun daukaka kara ta yi watsi da dokar Shari'ar Musulunci na jihar Kano saboda ta sabawa kundin tsarin mulkin Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng