Jirgin Ƙasa Ya Take Wata Mata Mai Matsalar Kurumta Yayin Da Ta ke Neman Abin Da Za Ta Kula Da Yaranta
- Tsautsayi ya afka wa wata mata mai matsalar kurumta inda jirgin kasa ya nike ta a Itoki, Jihar Ogun kamar yadda manema labarai suka bayyana
- Wani ma’abocin amfani da Twitter ne ya bayyana labarin mara dadi a kafar ranar Laraba da yamma inda ya wallafa hotunan yadda ta yi raga-raga
- Matar ta je tashar jirgin kasan ne tana neman aiki don ta samu ta kula da yaran ta kamar yadda ta bayyana hakan a wata takarda da ta rike
Jihar Ogun -Jirgin kasa ya nike wata mata inda ta yi raga-raga a Itoki, cikin Jihar Ogun, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
An bayyana yadda matar ta je kan titin jirgin kasan Legas zuwa Ibadan inda jirgin ya bi ta kan wuraren tashar Agbado da ke Itoki.
Wani ma’abocin amfani da Twitter ya labarta yadda lamarin ya faru a kafar tare da wallafa yadda matar ta yi daga-daga.
An ruwaito yadda marigayiyar ta riko karamar takarda wacce ta bayyana cewa kurma ce ita kuma tana neman taimako don kulawa da yaran ta.
A takardar matar ta ce tana nema wa yaran ta ingantacciyar rayuwa
Kamar yadda ojozacheus247 ya wallafa a shafinsa:
“Wata kurma ta rasa ran ta a wata tashar jirgin kasa da ke Itoki, Jihar Ogun da yamman nan. Abin ban tausayin shi ne yadda matar take tsaka da neman taimako don kulawa da jaririn ta. Akwai wata karamar takarda da ta riko inda ta bayyana bukatunta.”
Takardar wacce marigayiyar ta ke rike da ita an mata lakabi da “Bukatar taimako don kulawa da yara na”.
Can kasan takardar an rubuta:
“Ina neman taimako daga wurin ku komin kankantar shi. Ba na da kudi kuma ni kurma ce, amma ina so yara na su samu rayuwa mai inganci nan gaba. Ba ni da aikin yi, ku taimaka min don in kula da kai na da iyali na. Allah ya taimaka muku yayin da ku ke taimaka mana.”
Har washegari da safe ba a dauke gawar matar ba
Daily Trust ta gano cewa har safiyar Alhamis ba a riga an dauke gawar ta ba.
Manajan kamfanin jirgin kasan Jihar Legas (NRC), Injiniya Jerry Oche ya tabbatar wa wakilin Daily Trust faruwar lamarin a jiya. Kuma ya ce NRC za ta dauke gawar yau ta mayar da ita ma’adanar gawawwakin da ke jihar.
Ya bayyana damuwar sa inda ya ce bai dace wani ya je kan titin jirgin kasa ba ko da kuwa jirgin yana kusa ko ba ya kusa.
Asali: Legit.ng