An yi jana'izar DPOn yan sandan da yan bindiga suka kashe a Jibia
- Yan bindiga sun hallaka DPO na yan sanda da wani matashin hafsan Soja a garin Magamar Jibia
- Jami'in dan sandan ya rasa rayuwarsa ne yayinda ya jagoranci rundunar dakile yan bindigan da suka kai hari garin
- Jami'n Soja guda da ya samu rauni na kwance a asibiti kuma an ce yana murmurewa
Kano - An yi jana'izar DPO na yan sanda na karamar hukumar Jibia, DSP Abdullahi Rano, da ya rasa ransa a jihar Katsina.
Majiyoyi a hedkwatan yan sanda sun bayyana cewa an tafi da gawarsa jihar Kano domin yi masa jana'iza ranar Laraba.
Kakakin hukumar yan sandan jihar SP Gambo Isah ya yi alhinin mutuwar abokin aikinsa.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Mun kawo muku cewar tsagerun yan bindiga masu garkuwa da mutane sun kuma kai hari karamar hukumar Jibiya dake jihar Katsina da daren Talata, 8 ga watan Febrairu, 2022.
Yan bindigan sun hallaka DPO na ofishin yan sandan Magamar Jibiya da kuma wani hafsan Soja.
Hakazalika an ruwaito cewa wani kwamandan Soji ya jikkata.
Wannan ya faru ne lokacin da jami'an tsaron suka kai dauki cikin dare bayan samun labarin cewa yan bindiga sun shiga magamar Jibia suna harbe-harbe.
Mataimakin hakimin garin Mazanya, Abubakar Sani, ya tabbatar da harin.
Wani dan garin Magama-Jibia, Nura Magama, yace:
"Suna dira karfe biyun dare suka fara harbi har sai da aka kira Sallar Asuba. Abinda ya faru shine yan bindigan sun dira cikin motocin J5 da Sharon, inda sukayi musayar wuta da jami'an tsaro."
Karamar hukumar Jibia na daya daga cikin kananan hukumomin dake fuskantar barazanar yan bindiga a jihar Katsina.
Yan bindiga sun kashe Hakimi da wasu jama'arsa a jihar Katsina
Haka a ranar Alhamis, 3 ga watan Febrairu, 2022 yan bindiga masu garkuwa da mutane suka dira garin Yangayya dake karamar hukumar Jibia a jihar Katsina cikin dare.
Premium Times ta ruwaito cewa yan bindiga sun kashe Dagacin garin tare da mutum hudu.
Wani mazaunin Jibia, Halilu Kabir, ya bayyanawa manema labarai cewa yan bindigan sun kwashe sa'o'i uku suna cin karensu ba babbaka.
Asali: Legit.ng