Mataimakin Gwamnan Zamfara Ya Yi Babban Rashi, Matawalle Ya Yi Masa Ta’aziyya
- Alhaji Tukur Mai-Bulo, kawun mataimakin gwamnan Jihar Zamfara, Alhaji Mahdi Gusau ya riga mu gidan gaskiya
- Bello Matawalle, gwamnan Jihar Zamfara ya kai ziyarar ta'aziyya gidan marigayin tare da wasu jiga-jigan gwamnatin Jihar Zamfara
- Matawalle ya bayyana rasuwar Tukur Mai-Bulo a matsayin babban rashi ga al'ummar jihar kasancewarsa mutum wanda ya sadaukar da rayuwarsa don hidimtawa al'umma
Zamfara - Gwamna Bello Matawalle na Jihar Zamfara a ranar Laraba ya bayyana mutuwar Alhaji Tukur Mai-bulo, dattijon kasa, dan kasuwa kuma mai tallafawa al'umma a matsayin babban rashi a jihar.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a yau yayin da ya kai ziyarar ta'aziyya gidan marigayin wanda ya rasu a ranar Talata a Gusau, The Punch ta ruwaito.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Mai-Bulo, mai shekaru 72, kanin Janar Aliyu Gusau, kuma kawun mataimakin gwamna, Alhaji Mahdi Gusau ya rasu ne a ranar Talata ya bar matan aure uku da yara 25 da jikoki masu yawa.
Alhaji Tukur Mai-Bulo ya sadaukar da rayuwarsa wurin hidimtawa al'umma, Matawalle
Matawalle ya bayyana mutuwar Mai-Bulo a matsayin mutum mai tallafawa al'umma, mai gaskiya da rikon amana kuma mutum wanda ya bada gudunmawa sosai domin cigaban jihar, NewsWireNGR ta ruwaito.
Gwamnan ya ce marigayin ya shafe rayuwarsa wurin tallafawa al'umma.
A cewar gwamnan, za a yi kewar marigayi Mai-bulo saboda taimakon da ya ke yi wa al'umma.
Gwamnan ya yi addu'a Allah ya jikan marigayin ya bawa iyalansa damar jure rashinsa.
Matawalle ya mika ta'aziyyarsa ga iyalan mamacin da mutanen masarautar Gusau bisa rasuwar mammacin.
Wadanda suka yi wa gwamnan rakiya yayin ziyarar ta'aziyyar
Tsohon gwamnan Zamfara, Ahmed Sani, tsohon kakakin Majalisar Zamfara kuma Shugaban Ma'aikatan Kakakin Majalisar Wakilai na Kasa, Alhaji Sanusi Rikiji suna daga cikin wadanda suka yi wa gwamnan rakiya.
Sauran sun hada da Sakataren gwamnan jihar, Alhaji Kabiru Balarabe, Shugaban Ma'aikatan Fadar Gwamnan Zamfara, Malam Ibrahim Suleiman, Shugaban APC na Zamfara, Alhaji Tukur Danfulani da wasu manyan ma'aikatan gwamnati.
Mahaifiyar ɗan majalsa ta rasu awa 24 bayan raba wa matan da mazajensu suka rasu kuɗi da kayan abinci
A wani rahoton, mahaifiyar Dan Majalisar Wakilai na Tarayya kuma tsohon dan takarar gwamna a karkashin jam'iyyar All Progressives Grand Alliance, APGA, a Jihar Anambra, Chuma Umeoji, ta rasu, rahoon The Punch.
Mahaifiyar dan majalisar, Ngozi Umeoji, ta rasu ne a ranar Lahadi, a kalla awa 24 bayan ta raba wa matan da mazajensu suka rasu shinkafa, kudi da kayan abinci a garinsu a Ezinifite, karamar hukumar Aguata.
Asali: Legit.ng