Tarihi a 2022: Manya-manyan laifukan kashe-kashen tsafi 4 da suka girgiza 'yan Najeriya
Lamarin kashe-kashen mutane domin kudin asiri na kara hauhawa a kasar a yan baya-bayan nan. Duk da cewar ana cikin wata na biyu da shiga sabuwar shekara, an fuskanci kisa masu tayar da hankali a tsakanin matasan da ke son ganin sun yi kudi ta kowani hali.
Legit.ng ta tattaro wasu daga cikin kashe-kashen tsafi da suka afku a kasar cikin shekarar nan ta 2022.
1. Sofiat Kehinde
A ranar 4 ga watan Fabrairu, an tuhumi wasu matasa hudu a kan kisan wata matashiyar budurwa mai shekaru 20 a duniya.
An kama matasan wadanda shekarunsu ke tsakanin 18 zuwa 20 a karshen watan Janairu bisa zargin kashe Sofiat Kehinde da kuma kona kanta don yin kudi a yankin Oke Aregbe da ke Abeokuta, jihar Ogun.
A bisa rahotanni, matashiyar na soyayya da daya daga cikin makasan nata. Saurayin nata, Soliu, shine ya ja ta dakinsa inda suka far mata sannan suka kashe ta.
2. Timothy Odeniyi
A ranar 1 ga watan Fabrairun 2022, jami’an tsaro na Amotekun sun kama wani da ake zargin mai kisa don asiri ne, Timothy Odeniyi a jihar Ondo. Mutumin mai shekaru 35 ya sanar da manema labarai cewa an yi masa alkawarin naira miliyan 30 idan har ya iya kawo sassan jikin mutum a Lagas.
Ya bayyana cewa za a kaiwa wani uban gidansa da ke Lagas sassan jikin ne. Timothy ya bayyana cewa ya je makabarta ne ya tono sassan jikin gawawwakin da aka binne inda ya yi ikirarin cewa bai kashe kowa ba.
3. Jennifer Anthony
A lamarin Jennifer Anthony; yan sanda sun kama wani matashi dan shekara 20, Musa Oko bisa zargin kashe ta don asiri.
An tsinci Jennifer, wacce ta kasance daliba a jami’ar Jos mace a wani otel da ke Jos, a hanyar Zaria Road, a ranar sabuwar shekara.
Hakazalika babu wasu daga cikin sassan jikinta. An kama Moses a jihar Benue bayan ya tsere daga Jos, saboda laifin da ya aikata.
4. Afeez Olalere
Wani lamari kuma shine na Afeez Olalere mai shekaru 32, wanda ake zargin dan damfara ne ta yanar gizo.
Afeez ya tona cewa ya kashe kaninsa domin yin kudin asiri. Jami’an yan sanda ne suka kama shi a Lagas a yayin aikin bincike a hanyar Itamaga, Ikorodu.
Afeez ya ce mahaifiyarsa ce ta karfafa masa gwiwar kashe kanin nasa bayan wani boka ya fada masu sai an kashe rai kafin ya samu kudi kuma dole jininsa zai bayar.
Ya kitsa da mahaifiyarsa inda suka ba kaninsa guba ya ci sannan suka cire sassan jikin da ake so.
Asirin kuɗi zan yi da shi: Malamin da aka kama da sabon ƙoƙon kan mutum da ya siya N60,000
A wani labarin, wani wanda ya kira kansa malamin addinin musulunci mai shekaru 55, Tunde Olayiwola, ya amsa cewa ya siyo sabon kokon kan dan adama a Ajabbale, Oka a jihar Ondo, Vanguard ta ruwaito.
A hirar da ka yi da shi, wanda ake zargin da ya ce shi dan asalin garin Osogbo ne a jihar Osun, ya ce ya siya kokon kan ne kan kudi N60,000 domin a masa asiri, rahoton Blueprint.
Asali: Legit.ng