Sarauniyar kyau mai Hijabi: An nemi na cire Hijabi don na ci nasara, amma na tubure

Sarauniyar kyau mai Hijabi: An nemi na cire Hijabi don na ci nasara, amma na tubure

  • Shatu Garko, Sarauniyar kyan Najeriya ta 44 ta bayyana yadda ta fuskanci tarin kalubale saboda kasancewarta mai sanya hijabi
  • Budurwar mai shekaru 18 ta ce kamfanoni da dama sun ki yarda su yi aiki da ita a farkon fara harkarta saboda wannan hijabi nata
  • Ta ce harma wasu sun sha fada mata cewa ta cire hijabi idan har tana so tayi nasara amma bata bari hakan ya karya mata gwiwa ba

Matashiyar da ta lashe gasar kyau na Najeriya, Shatu Garko, ta magantu a kan gwagwarmayar da ta sha a farkon tafiyarta a matsayin ta na mai sanya hijabi.

Garko mai shekaru 18 a duniya, wacce ta lashe gasar na 44, inda ta lallasa abokan takara 18 wajen zama sarauniyar kyau mai hijabi ta farko ta bayyana hakan ne a wata hira da jaridar The Punch.

Kara karanta wannan

Kannywood: Isa ya yi martani kan hukuncin da kotu ta yankewa Sadiya Haruna kan batancin da ta yi masa

Sarauniyar kyau mai Hijabi: An nemi na cire Hijabi don na ci nasara, amma na tubure
Sarauniyar kyau mai Hijabi: An nemi na cire Hijabi don na ci nasara, amma na tubure Hoto: Punchng.com
Asali: UGC

Ta bayyana cewa da farko ta ji tsoro saboda hijabinta.

A cewarta, kamfanoni da dama sun ki aiki da ita saboda hakan inda tace suna bata shawarar da ta cire hijabin idan tana so ta yi nasara a harkar tallace-tallace.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Jaridar Punch ta nakalto Garko tana cewa:

“Na fara tallata kayan ado ne tsawon kasa da shekara daya. Bayan na kammala makaranta, ina garkame a gida saboda annobar korona. Na tsani zama haka babu aikin yi, sai na yanke shawarar gwada tallata kaya.
“Aikin farko da nayi ya kasance da tangarda. Da farko sun dauke ni amma sai daga baya suka ce ina bukatar jagoranci mai inganci sannan suka yi watsi da ni.
“Sai dai kuma, wannan bai karya mun gwiwa ba. Maimakon haka, ya karfafa mun gwiwar sake daura damara.
“Mahaifiyata ta fada mani, ‘ba zai yiwu ki yi nasara daga fara wannan abun ba’. Ta fahimtar da ni cewa dole sai mutum ya fadi kafin ya yi nasara.

Kara karanta wannan

Wani Saurayi ya lakadawa budurwarsa duka har ta mutu bayan ya dirka mata ciki

“A farkon fara aikin talla na, na dan tsorata saboda hijabina. An sha kin amsata saboda kamfanin basa son aiki da mai hijabi. A lokuta da dama, an sha fada mani na cire hijabina idan ina son yin nasara a harkar.”

Da kyar na shawo kan mahaifina ya bari na fito gasar sarauniyar kyau, Shatu Garko

A baya Shatu Garko, Sarauniyar kyau ta 44 a Najeriya ta shaida yadda ta samu nasarar shawo kan mahaifinta har ya amince ta shiga gasar.

Budurwar mai shekaru 18 ta zama mace ta farko mai hijabi da ta kashe gasar tun da aka fara a shekarar 1957 kamar yadda ta shaida wa The Punch a wata hira da jaridar ta yi da ita.

Ta kara da yadda ‘yan bani na iya suka dinga caccakar ta inda su ka dinga cewa zata kai Boko Haram cikin gasar, Punch ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng