Pantami, Fashola da sauran Ministocin da Majalisa ta gayyata kan binciken Kuɗi
- Kwamitin majalisar dokokin tarayya ya gayyaci Minsitocin shugaba Buhari hudu kan rahoton ofishin binciken kuɗi na kasa OAGF
- Kwamitin ta bakin shugabansa, Oluwole Oke, ya baiwa ministocin wa'adin mako ɗaya su tabbata sun zo sun yi bayani
- Ministocin sun hada da Fashola na ma'aikatar ayyuka da gidaje, da Rauf Aregbesola, na ma'aikatar harkokin cikin gida
Abuja - Kwamitin kula da asusun kuɗaɗen gwamnati na majalisar dokokin tarayya, jiya Talata, ya gayyaci ministocin Buhari hudu su gurfana a gaban shi.
The Nation ta rahoto cewa Kwamitin ya gayyaci ministocin ne domin su yi bayani kan rahoton binciken kuɗi na ofishin Audita Janar na ƙasa (OAGF).

Source: UGC
Mambobin majalisar dokoki dake cikin kwamitin na bukatar ministocin su yi ƙarin haske kan rahoton da OAGF ya fitar tsakanin 2016 da kuma 2019.
Hakanan kuma yan majalisun sun baiwa waɗan nan Ministoci wa'adin kwanaki Bakwai kacal su kawo kan su.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Wane ministoci ne abun ya shafa?
Ministocin da lamarin ya shafa sune; Ministan ayyuka da gidaje, Babatunde Raji Fashola, ministan lafiya, Dakta Osagie Ehanire.
Sauran sun haɗa da, Ministan harkokin sadarwa da tattalin arziƙin zamani, Farfesa Isa Ali Pantami, da kuma Ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola.
Shugaban kwamitin, Oluwole Oke, wanda ya baiwa mutanen wa'adi yayin zamansa, yace Ministocin su taho tare da Sakatarorin dindindin da kuma Daraktocin kuɗi na ma'aikatun su.
Meyasa suka sanya wa'adi?
Oke ya ƙara da cewa sanya wa'adin bayyanar Ministocin ya zama wajibi biyo bayan ƙin amsa gayyatar da kwamitin ya aike musu a baya.
Kwamitin kula da asusun gwamnati na ɗaya daga cikin kwamitocin da kwansutushin ya tanadar wa majalisar dokoki, kuma babban aikin shi, shi ne bin ƙwaƙƙwafin rahoton ofishin OAGF na ƙasa.

Kara karanta wannan
Zaben 2023: Masu son kujerar Buhari basu san dumin da ke tattara da ita ba, inji Sanusi
A wani labarin kuma Gwamnonin arewa biyu sun garzaya fadar shugaban ƙasa, sun saka labule da Buhari
Shugaban gwamnonin APC kuma gwamnan jihar Kebbi, Atiku Bagudu, tare da gwamnan Jigawa, Muhammad Badaru, sun gana da Buhari
Gwamnonin sun ziyarci fadar shugaban ƙasa ne domin tattauna wa game da babban taron APC na ƙasa dake tafe a watan Fabrairu.
Asali: Legit.ng
