Gurbataccen man Fetur: FG na iya mayar da mai ga masu kawo shi, abun ya shafi lita miliyan 100 - Yan kasuwa

Gurbataccen man Fetur: FG na iya mayar da mai ga masu kawo shi, abun ya shafi lita miliyan 100 - Yan kasuwa

  • Hasashe sun nuna cewa gwamnatin tarayya na iya mayarwa da masu kawo mata mai daga kasar waje gurbataccen man da aka shigo da shi kasar
  • Masu siyar da mai sun ce kimanin lita miliyan 100 na gurbataccen mai da aka shigo da shi kasar
  • Wannan al'amari ya haddasa layi da karancin mai a wasu manyan birane na jihohin kasar ciki harda birnin tarayya Abuja

Wani rahoton jaridar Punch ya kawo cewa gwamnatin tarayya ta hukumar kula da man fetur na iya mayarwa masu kawo mata mai daga kasar waje gurbataccen man fetur da kamfanin man fetur na kasa (NNPC) ta shigo da shi kasar.

Masu siyar da mai sun kiyasta cewa kimanin lita miliyan 100 na gurbataccen man fetur aka shigo da su Najeriya, kuma kamfanin sayar da kayayyakin bututun mai, wani bangare na NNPC ya janye shi.

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: FG ta tabbatar da cewa an samu matsala, an sayarwa gidajen mai gurbataccen fetur

Gurbataccen man Fetur: FG na iya mayar da mai ga masu kawo shi, abun ya shafi lita miliyan 100 - Yan kasuwa
Kimanin lita miliyan 100 na gurbataccen man fetur aka shigo da shi kasar Hoto: Punch
Asali: Facebook

A rahoton Vanguard, hukumar NMDPRA ta bayyana cewa gwamnati ta janye kimanin lita miliyan 80 na gurbataccen man daga kasuwar cikin gida.

Janyewar ya haifar da gagarumin layin mai a Abuja, Lagas, Neja, Nasarawa da wasu jihohi da dama, yayin da dandazon jama’a suka kewaye yan tsirarun wajen siyar da mai da ke da kaya.

Gidajen mai da dama sun rufe a ranar Talata, 8 ga watan Fabrairu saboda rashin mai da za su siyar, yayin da yan kasuwar bayan fage suka mamaye manyan tituna a Abuja, suna siyarwa da masu ababen hawa da ke da ra’ayi.

An kuma tattaro cewa koda dai ana kokarin ganin an magance lamarin, yawan layi da karancin man fetur na iya kaiwa karshen makon nan.

Kara karanta wannan

Almundahanar kudin makamai N13.8bn: An hana tsohon shugaban Soji fita kasar waje

Hukumar ta NMDPRA ta bayyana a cikin wata sanarwa da ta fitar a Abuja, cewa an gano takaitaccen adadin man fetur mai dauke da sinadarin methanol fiye da yadda Najeriya ta bukata a man da aka shigo da shi.

FG ta tabbatar da cewa an samu matsala, an sayarwa gidajen mai gurbataccen fetur

A baya mun kawo cewa Gwamnatin tarayya ta bakin hukumar lura man feturin saman kasa NMDPR ta tabbatar da cewa an samu matsala wajen sarrafa man feturin da aka sayarwa gidajen mai.

Hukumar NMDPR ta bayyana hakan ranar Talata inda tace adadi sinadarin 'Methanol' dake cikin feturin ya yi yawa.

A jawabin da ta saki, ta bayyana cewa an gano dan kasuwan man da yake raba wannan mai kuma za'a hukuntasa yadda ya kamata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng