Da duminsa: Yan bindiga sun kashe DPO da Hafsan Soja a sabon hari a Jibia

Da duminsa: Yan bindiga sun kashe DPO da Hafsan Soja a sabon hari a Jibia

  • Yan bindiga sun hallaka DPO na yan sanda da wani matashin hafsan Soja a garin Magamar Jibia
  • Rahotanni sun bayyana cewa yan bindigan sun kai hari cikin daren Talata garin
  • Kawo yanzu dai ba'a san adadin wadanda suka rasa rayukansu ko akayi awon gaba da su ba

Katsina - Tsagerun yan bindiga masu garkuwa da mutane sun kuma kai hari karamar hukumar Jibiya dake jihar Katsina da daren Talata, 8 ga watan Febrairu, 2022.

TVCNews ta ruwaito cewa yan bindigan sun hallaka DPO na ofishin yan sandan Magamar Jibiya da kuma wani hafsan Soja.

Hakazalika an ruwaito cewa wani kwamanda Soji ya jikkata.

Wannan ya faru ne lokacin da jami'an tsaron suka kai dauki cikin dare bayan samun labarin cewa yan bindiga sun shiga magamar Jibia suna harbe-harbe.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun hallaka mutum 10, sun sace Hakimi a jihar Katsina

Karamar hukumar Jibia na daya daga cikin kananan hukumomin dake fuskantar barazanar yan bindiga a jihar Katsina.

Har yanzu, hukumar yan sanda basu saki jawabi kan kisan jami'ian tsaron ba.

Ku dakaci karin bayani..

Jibia, Katsina
Da duminsa: Yan bindiga sun kashe DPO da Hafsan Soja a sabon harin a Jibia
Asali: UGC

Yan bindiga sun kashe Hakimi da wasu jama'arsa a jihar Katsina

Haka a ranar Alhamis, 3 ga watan Febrairu, 2022 yan bindiga masu garkuwa da mutane suka dira garin Yangayya dake karamar hukumar Jibia a jihar Katsina cikin dare.

Premium Times ta ruwaito cewa yan bindiga sun kashe Dagacin garin tare da mutum hudu.

Wani mazaunin Jibia, Halilu Kabir, ya bayyanawa manema labarai cewa yan bindigan sun kwashe sa'o'i uku suna cin karensu ba babbaka.

Yace sun shigo kan babura kuma suka fara harbi. Yayinda suke bi gida-gida suka kashe mutum hudu da suke kokarin guduwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng