Kujerun 2023 na masu ilimi ne: Majalisa ta kawo doka kan 'yan takarar da basu da digiri
- Majalisar wakilai na duba kudirin doka na neman samar da cancantar ilimi a manyan kujerun siyasar kasar nan
- Kudirin dokar da 'yar majalisa daga jihar Ogun, Adewunmi Onanuga ta dauki nauyi ta zarce karatu na biyu a zaman majalisar a yau
- A halin da ake ciki, kudirin dokar da ba a tafka muhawara akanta ba tana neman a gyara sashi na 65, 106, 131 da 171 na kundin tsarin mulkin 1999
FCT, Abuja - Wani kudirin doka da ke neman daukaka darajar ilimi ga masu neman ofishin shugaban kasa ya tsallake karatu na biyu a zauren majalisar wakilai.
Jaridar TheCable ta ruwaito cewa, kudurin dokar da ke neman gyaran kundin tsarin mulkin da ya tsallake karatu na farko a ranar Talatar da ta gabata, ya kuma nemi a kara mafi karancin cancantar ilimi kan masu neman kujerun gwamna, dan majalisar jiha da na tarayya.
Da take magana a zauren majalisar yayin zaman majalisar a ranar Talata, 8 ga watan Fabrairu, Onanuga ta ce kara mafi karancin cancantar ilimi ga wadannan mukamai na siyasa zai fi shirya masu neman mukamai su yi abin da ya dace.
Sabon kudirin dokar wanda 'yar majalisar wakilai daga jihar Ogun, Adewunmi Onanuga, 'yar jam’iyyar APC ce ta dauki nauyinsa na neman sauya tsarin tsayawa takara a kasar nan.
Onanuga ta ce:
"Wannan ba kudiri bane da aka yi don tauye sha'awar 'yan Najeriya a fagen siyasa, a'a, kudiri ne da zai taimaki 'yan Najeriya su shirya tsaf domin gudanar da aikin da ya dace na shugabancin siyasa.
“Kamar yadda muka fara gani, gasar neman mukamai a matakin jihohi da na kasa na kara yawa.
"Duk da yake wannan yana da kyau a matsayin tsarin zabe na duniya, kuma zai iya zama mara amfani idan mutanen da ba su da cikakken shiri na ilimi, suka shiga wadannan ofisoshin siyasa."
'Yar majalisar ta ce kudirin idan aka amince da shi ya zama doka, zai habaka ingancin ‘yan takarar da ke neman mukamai a kasar.
Ta kara da cewa yin karatu har zuwa jami'a zai baiwa dan takara ilimi, kwarewa da kuma kyakkyawan shirin iya shugabanci nagari.
Kudirin wanda bai sha doguwar muhawara ba, an amince da shi gaba daya ne lokacin da mataimakin kakakin majalisar Idris Wase ya sanar da tsallakewarta karatu na biyu.
Wasu ‘yan takara za su fuskanci matsala a 2023, ana neman gyara dokar shiga takara
Yayin da ake shirin zaben 2023, shugaban majalisar wakilan tarayya, Femi Gbajabiamila ya ce akwai bukatar a gyara dokar tsayawa takara a Najeriya.
Jaridar Daily Trust ta fitar da rahoto a ranar Talata, 18 ga watan Junairu, 2022 cewa Rt. Hon. Femi Gbajabiamila yana so a canza sharadin neman shugaban kasa.
Rt. Hon. Gbajabiamila ya yi jawabi na musamman a laccar yaye dalibai da aka yi a jami’ar UNILAG, inda ya bijiro da maganar samun shugabanni masu ilmi.
Shugaban majalisar wakilan yana gani akwai bukatar a canza doka ta yadda ba zai yiwu a ce takardar sakandare kadai ake bukata wajen neman mukami ba.
A cewar Rt. Hon. Gbajabiamila, an kawo sashe na 131(d) na tsarin mulki ne a wani lokaci dabam a tarihin kasar nan, yana ganin wannan lokaci ya wuce a yanzu.
A wani labarin, majalisar dattijai a ranar Talata 8 ga watan Fabrairu ta zartas da wani kudiri na kafa karin makarantun lauyoyi a shiyyoyin kasar nan shida, Daily Trust ta ruwaito.
Hakan ya biyo bayan nazarin rahoton kwamitin majalisar dattijai mai kula da harkokin shari’a, ‘yancin dan Adam da kuma harkokin doka, wanda Sanata Opeyemi Bamidele (APC, Ekiti) ya jagoranta.
Rahoton The Nation ya kawo adadin makarantun da ake dasu kafin a amince da karin. Makarantun lauyoyi da ake da su a yanzu sune kamar haka:
Asali: Legit.ng