Tsadar mai: Bidiyo ya fallasa yadda ake sayar da gurbataccen mai a wani gidan mai
- Wani bidiyo ya jawo cece-kuce a kafafen sada zumunta tun lokacin da aka ga wani gidan mai yana matsa gurbataccen mai ga kwastoma
- Bidiyon ya nuna wani gidan mai, inda ake matsa mai a cikin wata gorar ruwa, tare da ganin launin man ba kamar yadda aka saba ba
- A Najeriya dai ana fama da karancin man fetur a gidajen mai, wannan yasa wasu ke ganin ba laifin masu gidan man bane
Legas - Yayin da 'yan Najeriya ke ci gaba da fuskantar tsadar rayuwa ta kowane bangare, wasu masu gidajen mai suna kara wa ciwon gishiri ta hanyar sayar da gurbataccen mai.
Wani bidiyon da ya yadu a kafafen sada zumunta ya bayyana lokacin da wani ma'aikacin gidan mai ke kokarin cika wata gorar ruwa da wani mai launin ja da ya yi kama da gurbatacce.
A bidiyon da Legit.ng Hausa ta samo a kan shafin Facebook na jaridar Punch, an ga man da ake dura wa gorar da launin da bai yi kama da na man fetur ko kalanzir ko gas ba, duk da cewa a gidan mai ne.
Hakazalika, jaridar ta shaida cewa, wannan bidiyon ya fito ne daga jihar Legas, amma har yanzu ba a gano wane gidan mai bane.
Kalli bidiyon:
Martanin 'yan Najeriya
A kasan bidiyon, jama'a da dama sun nuna damuwarsu, inda suka bayyana ra'ayoyinsu game da bidiyon. Ga kadan daga martanin:
Faith Nkemjika Ucheabuchi tace:
"Ba laifinsu bane...laifin NNPC ne...
"Idan kana zaune a Legas, za ka fahimci irin tsawon layin da gidajen mai ke tarawa a yanzu..Na ji labari da safiyar yau lokacin da ake fadin haka...to, akwai dai wasu kura-kurai.
Adekunle Amos yace:
"Ba gurbataccen mai bane, ko dai ruwa ya shiga tanki ko kuma an tace man a gida ne, sau daya na taba saya wa janareta na. Na ji tsoro ko zai bata min janareta amma abin mamaki, ya yi min aiki ninki uku na awa daya da nake sa ran zai yi. Mai ne da aka tace a gida ba wai gurbatacce ba. Na gode."
Silas Shentukwak yace:
"Kuma irin wadannan mutanen ne za su rika ihun rashin shugabanci nagari. Eh akwai rashin shugabanci nagari da rashawa amma muna da namu laifi a karan kanmu. Wani lokaci mun fi gwamnati laifi."
Felix Ikhizama yace:
"Shi ya sa suke son rufe kafafen sada zumunta...zamu ci gaba da tona asirin duk wannan rashin hankalin."
Cephas Chris Walker Rock yace:
"Tankin ne ya rube wannan ya sauya launi. Na yi imanin cewa dole sun gaya wa wadanda za su saya kafin a basu."
Mun shiga uku: Tsadar man fetur ya sa 'yan Najeriya kuka, sunyi zazzafan martani
A wani labarin, ‘yan Najeriya sun tafi shafukan sada zumunta domin nuna damuwa, bacin rai da kuma fusata kan karancin man fetur da ke kara ci gaba da dabaibaye wasu sassan kasar nan.
An ga dogayen layukan da aka yi a safiyar yau a wasu sassan Legas da Abuja, lamarin da ya sa masu ababen hawa kokawa da hawan farashin mai a daidai lokacin da matsalar karancin abinci ke kara kamari.
Wani mashahurin Fasto @Olubankoleidowu, ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa:
“Mun shiga uku! Wannan sabon karancin man fetur yana tunatar da mu wace shawara ya kamata mu yanke a 2023. ’yan Najeriya ku bi a hankali. Allah ba zai sauko daga sama domin ya muku yaki ba, shi ya sa ya ba ku kwakwalwa.”
Asali: Legit.ng