An sace suriki da 'yan uwan miji yayin taron sulhunta mata da miji

An sace suriki da 'yan uwan miji yayin taron sulhunta mata da miji

  • Wasu yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun sace mutane uku, biyu cikinsu yan gida daya yayin taro na sulhu
  • An kira taron ne a Imeama Mgbowo a karamar hukumar Awgu ta Jihar Enugu don yin sulhu tsakanin mata da mijinta
  • Majiyoyi daga unguwar sun bayyana cewa 'yan bindigan sun afka wa masu taron ne suna harbi kuma suka sace mahaifin yarinya da 'yan uwan miji su biyu

Jihar Enugu - An sace wasu mutane uku yayin taron 'yan uwa da aka shirya a Imeama Mgbowo a karamar hukumar Awgu ta Jihar Enugu.

Wadanda aka sace sun sun hada da wani mai harkar sayar da gidaje da filaye, Cif Frank Aziude; yayansa, Alphonsus Aziude; da kuma surukinsu, Mr Eric Onyia, rahoton The Punch.

Kara karanta wannan

Innalillahi: 'Yan bindiga sun sace matar mataimakin shugaban PDP, da wasu mutum 10 a Abuja

An sun sace suriki da 'yan uwan miji yayin taron sulhunta mata da miji
Yan bindiga sun yi awon gaba da suruki da 'yan uwan mata yayin taron sulhunta aure. Hoto: The Nation
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wasu majiyoyi daga unguwar sun shaida wa wakilin The Punch cewa lamarin ya faru ne a yammacin ranar Lahadi yayin da yan bindiga suka kai wa masu yin taron hari, suka rika harbe-harbe kafin su sace wadanda abin ya faru da su.

A cewar majiyoyin, an kira taron ne domin yin sulhu tsakanin diyar Aziude da mijinta kafin maharan suka afka musu.

Kawo yanzu maharan ba su nemi kudin fansa ba

Daga daga cikin majiyoyin ya bayyana wa wakilin majiyar Legit.ng cewa har yanzu maharan ba su tuntubi iyalan mutanen ba domin neman kudin fansa.

An yi kokarin ji ta bakin rundunar yan sandan Jihar Enugu amma hakan bai yiwu ba domin kakakin yan sandan, Daniel Ndukwe, bai amsa kirar da aka masa ba da sakon kar ta kwana har zuwa lokacin hada wannan rahoton.

Kara karanta wannan

Da duminsa: 'Yan ta'adda sun sace limamin cocin katolika, sun sheke kukunsa

'Yan Sanda sun kama 'hatsabibin mai garkuwa da mutane' kan kisar tsohon jami'in dan sanda

A wani labarin, rundunar ‘yan sandan Jihar Imo sun kama wani Deberechi Chukwu bisa zarginsa da halaka tsohon jami’in ‘yan sanda a yankin Mgbala da ke karamar hukumar Oguta a jihar, The Cable ta ruwaito.

Mike Abattem, jami’in hulda da jama’an rundunar ‘yan sandan jihar Imo, ya ce an kama wanda ake zargin ne yayin da yake yunkurin tserewa daga jihar.

Kakakin rundunar ya ce Chukwu yana daya daga cikin ‘yan gidan yarin da suka balle gidan gyaran halin Imo inda yace ya hada kai wurin kashe-kashen jami’an tsaro a jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164