Shekaru 70 kan karagar mulki: Sarauniyar Ingila ta kafa tarihin da aka jima ba’a gani ba

Shekaru 70 kan karagar mulki: Sarauniyar Ingila ta kafa tarihin da aka jima ba’a gani ba

  • Sarauniya Elizabeth II, ita ce sarauniya mafi dadewa a tarihin Burtaniya, ta hau karagar mulki a ranar 6 ga Fabrairu, 1952
  • Sarauniyar mai shekaru 95 tana da shekaru 25 yayin wata ziyarar masarauta a kasar Kenya lokacin da ta sami labarin mutuwar mahaifinta, King George VI
  • Tsohuwar sarauniyar ta fara bukukuwan cikarta shekaru 70 a mulki ta hanyar gayyatar gungun al'umma zuwa gidanta na Sandringham da ke Gabashin Ingila

A ranar 6 ga watan Fabrairun bana ne Sarauniya Elizabeth II ta cika shekaru 70 a kan karagar mulkin Burtaniya.

Jaridar New York Times ta ba da rahoton cewa wannan ci gaba ya sanya sarauniyar cikin rukunin da ba a cika gani ba a tarihi, inda tarihi ya rubuta cewa, wasu sarakuna uku ne kawai aka san sun yi mulki sama da shekaru 70.

Kara karanta wannan

'Yancin mata ne: Gwamnatin Buhari ta magantu kan batun hana sanya Hijabi a makarantun Kwara

Sarauniyar Ingila ta cika shekaru 70 a kan mulki
Shekaru 70 kan karagar mulki: Sarauniyar Ingila ta cika shekaru 70 tana mulki | Hoto: nytimes.com
Asali: UGC

Abin da ya faru daidai shekaru 70 da suka gabata

Kafar labarai ta CNN ta kara da cewa Elizabeth II, mai shekaru 95, ta zama sarauniyar Burtaniya ne bayan rasuwar mahaifinta King George VI a ranar 6 ga Fabrairu, 1952, yayin da take kasar Kenya a wani rangadi na kasa da kasa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A shekarar da ta gabata, sarauniyar ta samu labarin bakin ciki, inda aka sanar da ita mutuwar mijinta Yarima Philip, wanda ya rasu yana da shekara 99 a duniya.

Sarauniyar za ta yi bikin ranar cika shekarun cikin sirri kamar yadda aka saba, ba ta kallon hakan a matsayin wani abun yiwa biki.

An shirya cancanrewa da bikin kwanaki hudu na bukukuwan Jubilee Platinum awatan Yuni mai zuwa.

Wani mutum ya ci gyaran Saurauniyar Ingila a Turanci har waje 9

Kara karanta wannan

An kama wata mata a Kano tana yunƙurin sace yaro ɗan shekara 5 a hanyarsa ta zuwa makaranta

A wani labarin kuma, Mwalimu Joshua Njenga ya gano wasu kura-kurai a jawabin da fadar sarauniyar Ingila Buckingham Palace ta saki ranar Talata 9 ga Maris kan zargin wariyar launin fatan da surukar sarauniyar, Meghan Markle ta zargi yan gidan.

A ra'ayin da ya bayyana a shafinsa na Facebook, Njenga ya hararo kura-kuran da aka yi a jawabin da fadar tayi domin martani kan zargin.

A cewar Njenga, kura-kurai sun cika jawabin daga farko har karshe, har da wasu kalamai da bai kamata ayi amfani da su ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.