Wani mutum ya ci gyaran Saurauniyar Ingila a Turanci har waje 9

Wani mutum ya ci gyaran Saurauniyar Ingila a Turanci har waje 9

- Jawabin da fadar Sarauniyar Ingila ta saki ranar 9 ga Maris na da kura-kuran Turanci a fahimtar Mwalimu Njenga

- Wannan ba shi bane karo na farko da mutumin ke cin gyaran jama'a

- Ya bayyana cewa dalibansa sun bankado kura-kurai tara cikin jawabin sarauniyar

Mwalimu Joshua Njenga ya gano wasu kura-kurai a jawabin da fadar sarauniyar Ingila Buckingham Palace ta saki ranar Talata 9 ga Maris kan zargin wariyar launin fatan da surukar sarauniyar, Meghan Markle ta zargi yan gidan.

A ra'ayin da ya bayyana a shafinsa na Facebook, Njenga ya hararo kura-kuran da aka yi a jawabin da fadar tayi domin martani kan zargin.

A cewar Njenga, kura-kurai sun cika jawabin daga farko har karshe, har da wasu kalamai da bai kamata ayi amfani da su ba.

DUBA NAN: Sheikh Abdallah Pakistan ya kai karan Sheikh AbdulJabbar Kabara kotu

Wani mutum ya ci gyaran Saurauniyar Ingila a Turanci har waje 9
Wani mutum ya ci gyaran Saurauniyar Ingila a Turanci har waje 9
Asali: Facebook

DUBA NAN: An nada tsohon sarkin Kano, Sanusi Lamido, matsayin khalifan Tijjaniyya a Najeriya

Wannan abu da yayi ya baiwa mutane da dama mamaki inda wasu ke cewa lallai yayi karfin hali wajen yiwa masu yare gyara a yarensu.

"Zuwa ga fadar Buckingham, a darasin safiyar yau, mun tattauna kan banbancin rubutun sha'awa da kuma na izza, kuma mun yi amfani da jawabinku. Na bukaci dalibaina su sake rubuta jawabin ta hanyar amfani da rubutun izza. Ga abinda suka yi," Mwalimu Joshua Njenga.

Mutane da dama sun tofa albarkacin bakinsu a kafafen sada zumunta inda wasu da dama ke sukansa.

A wani labarin daban, wasu mazaunan garin Nsukka a karamar hukumar Nsukka, jihar Enugu, sun nuna damu wa a game da tashin da farashin man fetur ya yi a yau dinnan.

Jaridar Premium Times ta rahoto cewa ana saida litar fetur tsakanin N220 da N225 a gidajen mai a garin Nsukka, bayan sanarwar da aka yi a safiyar yau.

Mazauna wannan gari sun yi hira da hukumar dillacin labarai na kasa, NAN inda su ka tabbatar da cewa wasu gidajen mai da yawa sun ki fito wa aiki.

Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin uku yanzu tare da shararriyar jarida Legit.

Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng