Da duminsa: 'Yan ta'adda sun sace limamin cocin katolika, sun sheke kukunsa

Da duminsa: 'Yan ta'adda sun sace limamin cocin katolika, sun sheke kukunsa

  • Miyagun 'yan bindiga dauke da makamai sun kai farmaki wata majami'a da ke Chawai a karamar hukumar Kaura ta jihar Kaduna
  • Miyagun sun kai mummunan farmakin a ranar Lahadi da dare inda suka sace limamin cocin Joseph Shekari
  • Ba su tsaya nan ba, a yayin farmakin sun halaka wani wanda ke taimaka wa limamin cocin da girke-girke

Kaduna - Wasu miyagu da ake zargin 'yan bindiga ne, sun kai hari majami'ar katolikan da ke Chawai a karamar hukumar Kaurun jihar Kaduna a daren Lahadi.

A farmakin ne suka yi garkuwa da wani malamin addinin kirista bayan sun hallaka daya daga cikin ma'aikatansa.

Vanguard ta ruwaito cewa, 'yan ta'addan sun yi garkuwa da fasto Joseph Shekari, amma ba su bar wani mai girkin gidan da ransa ba, wanda har yanzu ba a bayyana sunan sa ba, inda suka hallaka shi yayin kai harin.

Kara karanta wannan

Dalibin Bethel ya ce ba zai dawo gida ba, 'yan bindiga na gwangwaje shi da ababen duniya

Da duminsa: 'Yan ta'adda sun sace limamin cocin katolika, sun sheke kukunsa
Da duminsa: 'Yan ta'adda sun sace limamin cocin katolika, sun sheke kukunsa. Hoto daga Vanguardngr.com
Asali: UGC

Dalibin Bethel ya ce ba zai dawo gida ba, 'yan bindiga na gwangwaje shi da ababen duniya

A wani labari na daban, dalibin da shi kadai ya rage hannun masu garkuwa da mutane dan makarantar Bethel Baptist, ya yi mursisi ya ki dawowa gida, inda ya bayyana yadda yake jin dadin zama da 'yan ta'addan.

Sai dai, 'yan bindigan sun damke mamban kungiyar kiristocin Najeriya (CAN), wanda ya kai kudin fansar da 'yan ta'addan suka bukata bayan ya kai musu sakon, Vanguard ta ruwaito.

Shugaban kungiyar kiristocin Najeriya (CAN) a jihar Kaduna, Rev Joseph John Hajab, da mataimakin kungiyar a arewa, sun nuna damuwar su saboda ganin yadda "Dalibin da shi kadai ya rage, kuma mafi kankanta daga cikin wadanda aka yi garkuwa da su, yayi watsi da tayin da aka yi masa na samun 'yanci daga hannun yan ta'addan."

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Jami'an tsaro sun yi nasarar dakile mummunan harin yan bindiga a Zamfara

Idan za'a tuna, an yi garkuwa da dalibai 121 na makarantar Bethel Baptist a 5 ga watan Julin 2021 a harabar makarantar da ke kan titin Kaduna zuwa Kachia a Dishi a karamar hukumar Chikun da ke jihar Kaduna, amma daga bisani aka saki guda 120.

"Dalibin da ya ragen ya zabi ya zauna da 'yan bindigan, hakan ya matukar ba dukkan mambobin Baptist da gaba daya kungiyar CAN mamaki. An gano yadda 'yan bindigan suke gwangwaje shi da ababen duniya a duk lokacin da suka dawo daga harkallar su, hakan yasa yayi watsi da tayin 'yancin da aka mishi," a cewar Hayab.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng