Cin bashin Buhari: China ta fara jinkirta bashi, amma gwamnati na neman rancen N5.9tr

Cin bashin Buhari: China ta fara jinkirta bashi, amma gwamnati na neman rancen N5.9tr

  • Gwamnatin Najeriya na ci gaba da neman rancen kudade domin ci gaba da ayyukan more rayuwa, inji ministan sufuri
  • Wannan na zuwa ne daidai lokacin da kasar ke fama da matsin tattalin arziki da karancin kudaden shiga
  • Tuni gwamnati ta yanke shawarar neman rance daga kasashen Turai domin cike gurbin rancen da bata samu daga Sin ba

FCT, Abuja - Yayin da Sin ke sanya wajen ba gwamnatin Buhari bashi, gwamnatin tarayya na karkata zuwa kasuwannin Biritaniya inda take sa ran za ta ci bashin akalla dala biliyan 14.4 (kimanin Naira Tiriliyan 5.993) domin yin wasu ayyukan layin dogo.

Tuni dai rahotanni suka ce Bankin Standard Chartered ya amince da bayar da lamuni na dala biliyan 3.02 (N1,256tr) don gudanar da ayyukan. Alamu na nuni da cewa irin wannan matakin na iya rage cin bashi daga Sin, inji rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Sana'a goma: Yadda Dangote ya samu N217.5bn cikin kasa da sa'o'i , ya haura zuwa matsayi na 91 a duniya

Gwamnatin Buhari kan batun rancen kudi
Kasar Sin na jinkirin ba FG bashi, an fara neman hanyoyi a kasashen waje | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Najeriya na neman rancen dala biliyan 14.4 daga Turai

Najeriya na neman rancen dala biliyan 14.4 na aikin layin dogo da za a yi daga Fatakwal zuwa Maiduguri da kuma aikin layin dogon Kano zuwa Maradi (Nijar), kamar yadda Amaechi ya shaidawa Bloomberg a watan Yunin bara.

A cewar Darakta Janar na ofishin kula da basussuka (DMO), Patience Oniha, rancen da kasar Sin ta ba Najeriya, ba su da wata kadarar kariya akansu.

Ya zuwa ranar 30 ga Satumba, 2021, lamunin Sin ga Najeriya ya kai dala biliyan 3.59, wanda ke wakiltar 9.4% kawai na jimillar bashin da kasashen ketare ke bin gwamnatin Najeriya na dala biliyan 37.9.

A cewar Oniha:

“Jimillar bashin da ake bin Najeriya a ranar 30 ga watan Satumba ya kai dala biliyan 37.9, wannan adadi ya hada da bashin waje na gwamnatin tarayya, na gwamnatocin jahohi 36 da kuma babban birnin tarayya.”

Kara karanta wannan

Boka da magani: Yadda wata bokanya ke samun N1.8m a rana, ta mallaki makeken gida

A cewar wani rahoton kamfanin dillancin labarai na Reuters, Najeriya ta tuntubi bankin Standard Chartered Bank domin samun rancen ayyukan layin dogo guda biyu.

Ministan Sufuri Rotimi Amaechi ya ce hakan ya biyo bayan tsaikon da aka samu daga masu ba da lamuni na kasar Sin.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mayar da inganta hanyoyin sufuri da inganta tsofaffin hanyoyin samar da wutar lantarki ginshikin gwamnatinsa.

A bayyanawar gwamnati, hakan na nufin bunkasa harkar noma da sauran masana’antun da ba na man fetur ba, domin rage dogaro ga kudaden shiga na danyen mai. Amma har yanzu kudaden shiga ne babban cikas na gwamnatin Buhari.

Majalisar dokokin kasar nan a bara ta amince da karbo rancen biliyoyin daloli daga Sin da sauran masu ba da rance domin wasu ayyuka, amma har yanzu kudaden ba su cika ba.

Ya shaida wa manema labarai a Abuja cewa:

"Har yanzu muna jiran Sin su ba mu rancen da muka nema amma suna ta jinkirta lamarin."

Kara karanta wannan

Dukiyar sata: Yadda Ministan Buhari ya lallaba, ya ba kamfani kwangilar makudan Biliyoyi

“Za mu jira su ne har abada? Amsar ita ce a'a."

Kudaden da ake sa ran samu daga kasashen Turai

A watan Yunin 2021, Amaechi ya ce Standard Chartered ya amince da samar da dala biliyan 3.02 don aikin layin dogon Fatakwal zuwa Maiduguri.

Ya kuma ce a lokacin ana sa ran kamfanin Credit Suisse zai dauki nauyin aikin layin dogon Kano zuwa Maradi a Nijar wanda zai hada jihohin Arewa masu Yamma na Kano da Jigawa da Katsina.

Ministan ya kara da cewa:

“Mun je bankin Standard Chartered. Ba su yi rufa-rufa kan kudade ba, amma sun amince da wani daukar nauyin aikin layin dogo na Kano-Maradi."

Tagaiyararrun hanyoyin sufuri da wutar lantarki a Najeriya sun kawo cikas ga ci gaban tattalin arziki shekaru da yawa, tare da dakile habakar tattalin arzikin kasar, inda 40% na al'ummar kasar ke rayuwa cikin kangin talauci.

Amaechi ya ce majalisar zartaswa ta amince da a ba da dala miliyan 187.7 ga ‘yan kwangila da za su kula da ayyukan layin dogo uku ko hudu na ayyukan, kamar yadda kafar labarai ta ReubenAbati ta tattaro.

Kara karanta wannan

Kasar Sin ta hana mu bashi, yanzu Turai zamu je nema: Gwamnatin Tarayya

Shi ma da yake nasa jawabi, kwararre kan tsare-tsaren ababen more rayuwa, Okoli Ochuwa, ya bayyana cewa matakin da Najeriya ta dauka na komawa ga sauran kasashe masu ba da lamuni abin yabawa ne.

A cewarsa:

"Ko da yake a halin yanzu, bashin kasar Sin ba abin damuwa ba ne tukuna a Najeriya, amma idan muka ci gaba da dogaro da su, ba za mu iya samun mafita ba."

Bashin da ake bin Najeriya ya kara mummunan tashi a 'yan watanni

A wani labarin, jimillar bashin da ake bin Najeriya ya tashi daga N32.9tn a watan Disambar 2020 zuwa N39.6tn a watan Nuwamba 2021, inji rahoton jaridar Punch.

Ministar kudi, Misis Zainab Ahmed, a yayin gabatar da kasafin kudin shekarar 2022, ta bayyana cewa gwamnati ta ciyo bashin N6.7tn tsakanin watan Janairu zuwa Nuwamba 2021, kamar yadda kwafin gabatarwar ta bayyana.

Sabon rancen ya kunshi bashin gida N5.1tn da kuma N1.6tn da lokuta daban-daban. Sai dai bashin cikin gida ya hada da karbar rance daga babban bankin Najeriya kamar yadda takardar gabatar ta nuna.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Ɗan Kwamishiniyar Ganduje a jihar Kano ya ɓace

A watan Maris na 2021, Ofishin kula da basussuka ya bayyana cewa jimillar bashin da ake bin kasar ya kai N32.9tn a watan Disamba 2020.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.