Nasara: Yan bindiga sun kwashi kashin su a hannu yayin da suka kai hari Ofishin yan sandan Kogi
- Gwamnatin jihar Kogi ta tabbatar da cewa wasu yan bindiga sun kai hari babban ofishin yan sanda dake Okene a jihar Kogi
- A sanarwar da kwamishinan labarai, Kingsley Fanwo, ya fitar yace an kashe mutum ɗaya daga cikin su, sauran sun gudu da raunuka
- Kwamishinan ya yi kira ga al'ummar jihar su gaggauta kai rahoton duk wanda suka gani da raunin harbin bindiga
Kogi - Yan bindiga sun farmaki Ofishin yan sanda dake yankin Okene, jihar Kogi jiya Lahadi da yammaci, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.
Yan ta'addan sun haura 30, a cewar wata sanarwa da kwamishinan watsa labarai na jihar, Kingsley Fanwo, ya fitar, yayin da yake tabbatar da aukuwar lamarin.
Fanwo yace ɗaya daga cikin yan bindigan ya gamu da ajalinsa yayin da sauran suka ranta a na kare ɗauke da raunin alburushi a jikkunan su.
Daily Trust ta rahoto Sanarwan tace:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Gwamnatin Kogi ta samu rahoton kai hari babban Ofishin yan sanda dake Okene, wanda wasu yan bindiga sama da 30 suka kai da yammacin ranar Lahadi 6 ga watan Fabrairu, 2022."
"An nuna musu karfi da kuma dabarun aikin tsaro na jihar Kogi, yayin da Mafarauta, Yan Bijilanti tare da haɗin kan sauran hukumomin tsaro suka daƙile harin."
"Luguden wutan da suka sha ya sa aka bindige ɗaya daga cikinsu har lahira, saura suka gudu da raunuka. Jami'ai sun kwato Babura biyu, Bindigu da alburusai daga hannun su."
Wannan shi ne karo na biyu da yan bindiga suka kwashi kashin su a hannu, inda aƙalla yan bindiga 10 suka sheƙa lahira yayin da suka kai hari Yagba West a watan Disamba.
Shin an kashe mutane a harin?
Kwamishinan ya ƙara da cewa babu wanda ya rasa rayuwarsa a harin, sai dai yan ta'addan da suka tsere da harbin bindiga a jikinsu, kuma ɗayan su ya mutu a wurin musayar wuta.
Ya yi kira ga Sarakuna da al'umma baki ɗaya su gaggauta kai rahoton wanda suka gani da raunin bindiga ga hukumomin tsaro mafi kusa.
Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya sha alwashin cewa duk yan bindigan da suka shigo jihar ba zasu fita da rayuwarsu ba.
A wani labarin kuma Mutanen gari sun fusata, sun aika yan bindiga biyu Lahira yayin da suka kai hari
Mutanen gari sun samu nasarar kama wasu yan fashi da makami da suka addabi yankin su, kuma ba su yi wata-wata ba wajen aika su lahira.
Wani shaida ya bayyana cewa an kama mutum biyu daga cikin yan fashin yayin da suka shiga wani garejin gyaran mota a Legas.
Asali: Legit.ng