Buhari ya bi ayarin malaman addinai, ya hada ASUU da Allah da Annabi kada su tafi yajin aiki
- Shugaba Muhammadu Buhari ya fara makon da ya gabata ne da alkawarin cewa gwamnatinsa za ta karrama alkawarin da ke tsakanin ta da ASUU
- A cewar shugaban kasar, babu wata kasa da za ta ji dadin ganin cewa fannin iliminta ya tabarbare, don haka za a inganta fannin
- Buhari ya sanar da hakan ne yayin da ya karba bakuncin shugabannin addinai karkashin jagorancin Mai Alfarma Sarkin Musulmi da shugaban CAN
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya fara makon da ya gabata da shan alwashin cewa gwamnatin tarayya za ta karrama alkawarin da ta yi wa kungiyar malamai masu karantarwa ta jami'o'i, ASUU.
Shugaban kasan ya ce hakan zai hana wani yajin aiki tabbata, ya tabbatar da cigaban karatu da kuma inganta karatu a manyan makarantu, Daily Nigerian ta ruwaito hakan.
Shugaban kasan ya yi wannan batun a ranar 1 ga watan Fabrairu, yayin da ya karba bakuncin shugabannin addinai wadanda suka samu shugabancin Mai alfarma Sa'ad Abubakar II da shugaban CAN, Samson Ayokunle.
ASUU a ranar Juma'a ta bayyana tantamar ta kan cewa gwamnatin tarayya za ta iya shawo kan matsalar bangaren ilimi a kasar nan, ballantana a jami'o'i inda ta ke barazanar cewa kungiyar babu dadewa za ta fada yajin aiki.
Daily Nigerian ta ruwaito cewa, sai dai kuma, shugaban kasar ya ce babu wata al'umma da za ta nuna halin ko in kula ga bangaren ilimi da sassan ta.
A don hakan, ya jinjina wa shugabannin NIREC kan yadda suka shiga lamarin da kuma yadda ta dinga tattaunawa da dukkan bangarori.
ASUU ga FG: Ba za ku taba samun kwanciyar hankali ba, har sai mun sasanta
A wani labari na daban, kungiyar malamai masu koyarwa na jami'o'i, ASUU, a jiya ta sanar da gwamnatin tarayya cewa ba za ta samu kwanciyar hankali ba har sai ta sasanta da su kan halin da ilimin jami'o'i ke ciki.
A wata zantawa da manema labarai a Awka, shugaban ASUU na jami'ar Nnamdi Azikiwe, Comrade Stephen Ofoaror ya ce ya gane yadda ake neman barazana ga zaman lafiyan kasar.
Vanguard ta ruwaito cewa, inda ya ja kunne a kan bakar guguwar da ta taso sanadiyyar gazawa wurin cika alkawarin da gwamnatin tarayya ta dauka na girmama yarjejeniyar da ta yi da ASUU a ranar 23 ga watan Disamba, 2020.
Asali: Legit.ng