Allah ya yiwa mahaifin tsohon kwamishinan yan sandan Kano ‘Singam’ rasuwa
- Mahaifin tsohon kwamishinan yan sandan jihar Kano, CP Muhammad Wakili, Alhaji Buba Turaki, ya rigamu gidan gaskiya
- Marigayin wanda ya kasance tsohon jami’in hukumar Kwastam na Najeriyan ya rasu a safiyar yau Lahadi, 6 ga watan Fabrairu
- Za a yi jana’izarsa da misalin karfe 2:00 na rana a kofar Fadar mai martaba Sarkin Gombe
Allah ya yiwa wani tsohon jami’in hukumar Kwastam na Najeriya, Alhaji Buba Turaki, rasuwa.
Marigayin wanda ya kasance mahaifi ga tsohon kwamishinan yan sandan jihar Kano, CP Muhammad Wakili wanda aka fi sani da Singam ya rasu a safiyar yau Lahadi, 6 ga watan Fabrairu, a jihar Gombe.

Source: UGC
Ya rasu yana da shekaru 106 a duniya bayan ya yi fama da rashin lafiya, jaridar Aminiya ta rahoto.
Alhaji Turaki ya rasu ya bar matan aure da ’ya’ya 10, maza biyar da mata biyar.

Kara karanta wannan
Hadarin mota: Kwanaki bayan kammala digiri a ABU, matashi da mahaifiyarsa sun rasu a hadari
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Aminiya ta kuma rahoto cewa za a gudanar da jana’izarsa da misalin karfe 2:00 na rana a kofar Fadar mai martaba Sarkin Gombe.
Hadarin mota: Kwanaki bayan kammala digiri a ABU, matashi da mahaifiyarsa sun rasu a hadari
A wani labarin kuma, mun ji cewa Allah ya yiwa wani dalibin jami'ar Ahmadu Bella University (ABU), Zaria, wanda ya kammala karatu kwanan nan, Bashir Maiwada Zubairu, rasuwa.
A wani wallafa da shafin Instablog9ja ya yi a Instagram, an tattaro cewa Maiwada ya rasu ne tare da mahaifiyarsa a wani hatsarin mota.
Mummunan al'amarin ya afku ne a ranar Asabar, 5 ga watan Fabrairu, a hanyar Kano zuwa Katsina.
Asali: Legit.ng