Wata sabuwa: Fostocin takarar shugabancin kasa na Amaechi sun karade Daura
- Bayan nadin da Sarkin daura, Faruk Umar Faruk, ya yi wa ministan sufuri, Rotimi Amaechi, fostocin ministan sun karade titunan Daura
- Duk da a wurin nadin sarautar,Mai Martaba ya yi kira da Amaechi da ya nemi babban ofishin shugabancin saboda ya cancanta
- A cewar basaraken, Amaechi ya taka rawar gani wurin kawo jami'ar sufuri Daura kuma titin dogo na Kano zuwa Maradi zai ratsa ta Daura
Daura, Katsina - A jiya, Mai Martaba Sarkin Daura, Faruk Umar Faruk, ya roki ministan sufuri Rotimi Amaechi, wanda ya kwatanta da wanda ya cancanta da ya nemi mukami babba.
Basaraken ya mika wannan baukatar ne yayin karrama Amaechi da sarautar Dan Amanar Daura, Vanguard ta ruwaito.
Bikin nadin sarautar ya samu halartar manyan mutane a fadin kasar nan kuma masu kamfen ga ministan kan fitowa takarar zaben shugabancin kasa a 2023 sun cika garin da fostocin Amaechi.
Sarkin ya ce: "Mun hadu a nan domin mayarwa kura aniyar ta kan abubuwan arzikin da ministan sufuri, Chibuke Rotimi Amaechi ya ke mana na kauna da goyon baya.
"A don haka, ya zama wajibi ga masarautar Daura da ta yaba wa wannan goyon bayan. Ina fatan Ubangiji ya ba ka ofishin da ya fi wanda ka ke."
Faruk ya ce masarautar Daura ta bai wa Amaechi sarautar ne duba da gudumawar da ya ke bai wa cigaban kasar, ballantana wurin kafa jami'ar sufuri a Daura da kuma tabbatar da cewa titin dogo na Kano zuwa Maradi ya ratsa ta Daura, Vanguard ta ruwaito.
"Ba mu bayar da sarauta saboda kudi ba. Muna bayar wa ne duba da irin sadaukarwa da kuma rawar da ka taka wurin tallafawa rayuwar jama'a da kasar baki daya," basaraken yace.
Sarkin Daura: Ba mu bada sarauta don kuɗi, Amaechi ya cancanci naɗin da aka masa
A wani labari na daban, Mai martaba Sarkin Daura, Alhaji Umar Farouq, ya ce Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi ya cancani sarautar da masarautar Daura ta ba shi.
Farouq ya yi wannan jawabin ne a ranar Asabar yayin nadin sarautar da aka yi a Daura, Jihar Katsina, rahoton The Cable.
An karrama Amaechi ne da sarautar 'Dan Amanar Daura' yayin bikin nadin da manyan mutane da dama suka hallarta.
Asali: Legit.ng