Zamfara: 'Yan ta'adda sun sheke liman, wasu 32, sun sace mata da yara kan kin biyan N40m haraji

Zamfara: 'Yan ta'adda sun sheke liman, wasu 32, sun sace mata da yara kan kin biyan N40m haraji

  • Miyagun 'yan bindiga sun kai farmaki mabanbanta a kauyukan Yar Katsina, Nasarawar Mai Fara da Nasarawa duk a Zamfara inda suka kashe mutum 33
  • An gano vewa, Ada Aleru, gagararren shugaban 'yan bindiga ne ya saka wa jama'a harajin N40 miliyan amma suka gaza biya
  • A yayin da 'yan ta'addan suka shiga kauyen Yar Katsina, sun tarar ana sallar Juma'a amma suka hargitsa jama'a tare da halaka babban limami

Zamfara - 'Yan bindiga sun halaka sama da rayuka talatin, sun yi garkuwa da wasu mata a hari mabanbanta a ranar Juma'a duka a jihar Zamfara, Daily Trust ta ruwaito.

Yankunan da aka kai farmakin sun hada da Nasarawar mai Fara da ke karamar hukumar Tsafe, Yar Katsina a karamar hukumar Bungudu da kauyen Nasarawa da ka karamar hukumar Bakura.

Kara karanta wannan

Zamfara: Ƴan bindiga sun kashe mutum 33 saboda ƙin biyan harajin N40m da suka saka a wasu ƙauyuka

Zamfara: 'Yan ta'adda sun sheke rai 33 bayan sun gaza biyan harajin N40m da suka saka musu
Zamfara: 'Yan ta'adda sun sheke rai 33 bayan sun gaza biyan harajin N40m da suka saka musu. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Zamfara kamar sauran jihohin arewa maso yamma, ta na fama da rashin tsaro. Al'amuran 'yan bindigan kullum kara kamari su ke yi.

Dubban jama'a aka kashe kuma 'yan bindigan sun yi garkuwa da mutane masu yawa a yankin, lamarin da ya kara gaba har jihar Niger tun shekarar 2021.

A makonni uku na shekarar 2022, a kalla mutum 486 'yan ta'adda suka halaka a fadin Najeriya, rabi daga ciki kuwa duk a jihohin arewa maso yamma ne da jihar Niger.

An halaka rayuka 20 saboda sun kasa biyan haraji

Majiyoyi sun sanar da Premium Times cewa harin da aka kai Nasarawar Mai Fara da ke karamar hukumar Tsafe ya biyo bayan gazawar mazauna yankin ne wurin biyan harajin N40 miliyan da 'yan bindigan suka saka musu.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: 'Yan bindiga sun afka wa mutane a kan titi a Kaduna, sun kashe shida

Ada Aleru, wani gagararren shugaban 'yan bindiga da ke addabar yankin da Faskari a jihar Katsina ne ya saka harajin.

Abubakar Bala, wani mazaunin Tsafe, ya ce sun kasa hada harajin shiyasa miyagun suka kai musu farmakin.

An kashe babban limami

A yankin Bakura, wani ma'aikacin lafiya, Masud Kyambarawa ya sanar da Premium Times cewa an halaka mutum uku, ciki har da Akilu Dan Malam, babban limamin yankin.

Ya ce:

"Ina garin a lokacin da na fara jin harbi. Mun je dubawa, dole ta sa muka karasa kauyen Rabah a jihar Sokoto. Abu ne mara dadin kallo. Jama'a ballantana mata da kananan yara sun yi ta gudu zuwa daji domin tseratar da rayukansu.
"Mun gode Allah, a yanzu mun tsira amma na ji an ce sun halaka mutane uku."

A kauyen Yar Katsina da ke Bungudu, 'yan bindigan sun hana mutane yin sallar Juma'a.

Wata majiya wacce ta bukaci a boye sunanta saboda tsaro, ta sanar da cewa yayin da 'yan bindigan suka isa kauyen, jama'a lokacin suna Masallacin Juma'a amma suka tarwatsa su.

Kara karanta wannan

Da dumi: Yan bindiga sun kashe Hakimi da wasu jama'arsa a jihar Katsina

Zamfara: Sojoji da 'yan sanda sun ceto mutum 32 da 'yan ta'adda suka yi garkuwa da su

A wani labari na daban, rundunar hadin guiwan sojoji da 'yan sanda ta ceto mutane 32 da aka yi garkuwa da su daga bangarori daban-daban na jihar Zamfara.

Yayin zantawa da manema labarai a hedkwatar su da ke Gusau, Muhammad Shehu, mai magana da yawun yan sandan jihar Zamfara, ya ce wadanda aka ceto 'yan jihohin Neja, Katsina da Zamfara ne.

Shehu ya ce: "An kula da wadanda aka ceton yadda ya dace inda 'yan sanda suka musu tambayoyi sannan aka mika su ga iyalan su."

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng