Niger: 'Yan kauye ne ke bai wa 'yan ta'adda bayanan sirri, Sanata Musa

Niger: 'Yan kauye ne ke bai wa 'yan ta'adda bayanan sirri, Sanata Musa

  • Sanata mai wakiltar yankunan da 'yan bindiga suke cin karen su babu babbaka, ya nemi matasa da mazauna yankin da su hada kai don fatattakar yan ta'adda.
  • Sanatan ya bukaci gwamnatin tarayya ta samar da tabbataccen sansanin sojoji a yankunan da ake yawan kai hare-hare a jihar
  • An samu labarin yadda wasu mazauna kauyuka suka zama 'yan leken asiri ga yan bindiga, wanda hakan ke share wa yan ta'adda hanyar kai farmaki a yankunan

Niger - Sanata Sani Musa, mai wakiltar gabashin jihar Niger inda 'yan bindiga suke cin karen su babu babbaka, ya yi kira ga mazauna kauyuka da matasa da su hada kawuna don ganin an zakulo gami da wartakar 'yan bindiga a jihar Niger.

Ya kara da kira ga jami'an tsaron da su yi amfani da dabarbarun zamani wajen ganin sun yi gaba da gaba da 'yan ta'addan kamar yadda ya roki gwamnatin tarayya da ta samar da tabbataccen sansanin sojoji a yankunan da ake yawan kai hari, Vanguard ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: Gwamnatin Niger ta saka dokar hana fita a kananan hukumomi 2

Niger: 'Yan kauye ne ke bai wa 'yan ta'adda bayanan sirri, Sanata Musa
Niger: 'Yan kauye ne ke bai wa 'yan ta'adda bayanan sirri, Sanata Musa. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

Sanatan, yayin wata tattaunawar waya da jaridar Vanguard, ya sanar da yadda wasu al'amura marasa dadi suke faruwa a jihar, inda suke nuna yadda wasu 'yan kauye suke da hannu dumu-dumu a ta'addanci, har wasu suke zama 'yan leken asirin 'yan bindigan wanda hakan ke matukar wahalar da jami'an tsaro don ganin sun sheke su.

Musa ya ce, wannan ba lokacin siyasa ba ne, bayan tashin hankalin da ake ciki, lokaci ne da duk masu rike da mikamai za su hadu guri daya domin yakar bayyanannun makiyan.

"Wani lamari da ya faru kwanan nan ya bayyana yadda wasu mazauna kauye suka zama 'yan leken asiri ga 'yan bindiga, wanda hakan ke share musu hanyar kawo hari yankunan," a cewar Sanata.
"Ina rokon matasa musamman a yankunan da al'amarin ya shafa da su zakulo masu taimaka wa 'yan ta'adda kuma su kai karar su inda ya dace don a dauki mataki.

Kara karanta wannan

Katsina: An kama boka da ke yi wa 'yan bindiga asiri da addu'oin samun sa'a

"Ya kamata gwamnatin tarayya ta dauki matakin da ya dace don ganin ta samar da tabbataccen sansanin sojoji a yankunan da ta'addancin ya shafa, yayin da sojojin za su yi amfani da dabarbarun zamani wajen yin fito na fito da yakar hatsabiban".

An dauki tsawon shekaru ana musayar yawu tsakanin matasan yankunan da al'amarin ya shafa da gwamnati game da hare-haren da 'yan bindiga suke kai wa jihar.

Rashin tsaro: Gwamnatin Niger ta saka dokar hana fita a kananan hukumomi 2

A wani labari na daban, gwamnatin jihar Niger ta sa dokar ta baci na tsawon awa 24 a Shiroro da karamar hukumar Rafi saboda yawan hare-haren da 'yan bindiga suke kai wa yankunan.

Matakin da aka dauka sun biyo bayan rahotanin sirri da aka samu na cewa 'yan bindigan masu dumbin yawa za su kai farmaki cikin jihar, The Nation ta ruwaito.

An samu labarin yadda aka umarci mazauna Rafi da Shiroro da su zauna a gidajen su daga karfe 5:00 na yammacin Asabar har sai baba ta gani.

Kara karanta wannan

Nasara: 'Yan sanda sun halaka 'yan ta'adda 23, sun yi ram da 'yan bindiga 37 a Sokoto

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng