Katsina: Yan bindiga sun sake kai kazamin hari Malumfashi jihar Katsina, sun kashe mutane
- Yan ta'adda sun sake kai wani kazamin hari karamar hukumar Malumfashi dake jihar Katsina, arewa maso yammacin Najeriya
- Wata majiya da shaida mana cewa maharan sun farmaki ƙauyuka biyar a gundumar Karfi, sun kashe akalla mutum 17
- Ɗan majalisa mai wakiltar Malumfashi a majalisar dokokin jihar yace ya kai ziyara yankunan domin ta'aziyya ga mutane
Katsina - Yan bindiga sun kai wani kazamin hari gundumar Karfi, karamar hukumar Malumfashi, jihar Katsina jiya Jumu'a da daddare.
Daily Trust ta rahoto cewa yan ta'addan sun kashe akalla mutum 17, wasu da dama sun jikkata.
Majiya mai ƙarfi ta tabbatar da cewa yan bindigan sun farmaki aƙalla ƙauyuƙa biyar dake karkashin gundumar Karfi, suka buɗe wa mutane wuta kan mai uwa da wabi.
Leadership ta rahoto Majiyar tace:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Yan bindigan sun shigo da misalin ƙarfe 11:00 na daren ranar Jumu'a, suka buɗe wuta kan mazauna kauyukan kan mai uwa da wabi."
"Yayin haka sun kashe mutane 17 kuma sun saci kayyakin mutanen da basu ji ba su gani ba."
Ɗan majalisa ya tabbatar
Ɗan majalisa mai wakiltar ƙaramar hukumar a majalisar dokokin jihar Katsina, Aminu Ibrahim Saidu, ya tabbatar da aukuwar lamarin.
Yace tuni ya kai ziyara ƙauyukan da lamarin ya shafa domin yi wa iyalan waɗan da lamarin ya shafa ta'aziyya da jajanta musu.
Ana cigaba da samun karuwar hare-haren yan bindiga a jihar Katsina, wanda hukumar yan sanda ta alaƙanta haka da kwararar yan ta'adda daga jihohin Zamfara da Sokoto.
Rahoto ya nuna cewa luguden wutan sojojin Najeriya ta sama da ƙasa ya tilasta wa yan bindiga da dama tserewa daga sansanonin su.
A wani labarin na daban kuma Pantami ya faɗi babban abinda yan bindiga ke amfani da shi wajen ayyukan ta'addanci a Arewa
Minsitan sadarwa a Najeriya, Farfesa Isa Ali Pantami, yace yan bindiga na ribatar yawan faɗin kasa a jihohin arewa maso gabas wajen aikata ta'addanci.
Pantami yace hudu daga cikin jihohin Najeriya shida da suka fi faɗi duk suna yankin arewa maso gabas.
Asali: Legit.ng