Yaki da ta'addanci: Gwamna Zulum ya gwangwaje jami'an tsaro da kyautar motoci 18
- Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya gwangwaje jami'an tsaro da motocin sintiri a jiharsa ta Borno
- Ya mika kyautar motocin ne ga kwamandan Operation Hadin Kai a jihar Borno, inda ya kuma bude wasu hanyoyi
- Rundunar soji ta ji dadin wannan kyauta, ta tabbatar da goyon baya da ci gaba da aiki tukuru wajen wanzar da zaman lafiya
Jihar Borno - Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya mika kyautar motocin aiki ga jami'an tsaron hadin gwiwa da ke yakar ta'addanci a jihar Borno.
Yankuna da dama na fama da rashin tsaro a jihar Borno, musamman ganin yadda 'yan ta'addan Boko Haram da ISWAP ke addabar yankin Arewa maso Gabas.
Majiyar Legit.ng Hausa ta nuna hotunan motocin guda 18, tare da gwamnan da wasu jami'an tsaro yayin mika kyautar.
A cewar wata sanarwa da gwamnatin jihar ta fitar, gwamnan na Borno, ya ba da kyautar motocin sintirin ne domin karfafawa gwiwa fa sojoji, 'yan sa kai, mafarauta da ’yan banga da suka sadaukar da kai ga sintiri a hanyar Maiduguri-Dikwa-Gamboru.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Zulum ya mika motocin ga kwamandan Operation Hadin Kai, Manjo Janar Christopher Musa, yayin da yake kaddamar da shirin bude hanyar tattalin arziki ga matafiya a ranar Juma’a a kewayen Muna a Maiduguri.
Kalli hotuna:
Godiya daga gidan soji
A nasa bangaren, kwamandan Operation Hadin Kai, Manjo Janar Christopher Musa, ya yaba wa gwamnan, inda ya kuma jaddada kokarin gwamnan da jin dadin bude hanyoyin.
A cewarsa:
“A gare mu a matsayinmu na jami’an tsaro, hakika muna godiya. Ranka ya dade mun san wannan abu ne da ake so, kuma abu ne mai armashi kuma abu ne da kake so wa al’ummar Jihar Borno.
"Wannan wani bangare ne na kokarin samar da zaman lafiya, da wannan za a samu ci gaba, idan aka samu ci gaba za a samu raguwar kalubale kan tsaro."
Ya kuma jaddada goyon bayan jami'an tsaro wajen tabbatar da zaman lafiya ga a'ummar jihar Borno, inda yace:
"Za mu ba ku goyon bayanmu, hadin kan mu don ganin jihar Borno ta kasance cikin zaman lafiya da sauran sassan Arewa maso gabas domin rayuwa ta dawo daidai."
A wani labarin, shekaru uku bayan rufe titin Maiduguri-Dikwa-Mafa-Gamboru Ngala mai tsayin kilomita 137 sakamakon hare-haren Boko Haram, gwamnatin jihar Borno da Sojoji sun bude titin.
Gwamna Babagana Umara Zulum yayin bude titin ranar Juma'a ya jinjinawa Sojoji da yan sa kai bisa taimakon da suka bada wajen tabbatar da zaman lafiya a yankin, rahoton ChannelsTV.
Hakazalika ya yi kira ga direbobi su hada kai da jami'an tsaro wajen tabbatar da rayuwa da kasuwanci sun dawo hanyar.
An yi taron bude titin ne a Muna kuma Gwamnan ya hau titin har zuwa Dikwa domin tabbatar da cewa lallai an bude hanyar gaba daya.
Asali: Legit.ng